Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Nijeriya ta samu goyon bayan ƙasashe bakwai tare da alƙawuran ƙasashe 20 domin a kafa Cibiyar Koyar da Ilimin Yaɗa Labarai ta Duniya (IMILI) ta hukumar UNESCO.
Ita da UNESCO, ita ce Hukumar Ilimi da Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
- An Kashe Na Biyun Turji A Shugabanci Tare Da Fitattun Kwamandojin ‘Yan Bindiga A Zamfara
- Ba Mu Buƙatar Amincewar Sanusi Kan Tsare-tsarenmu Na Tattalin Arziki – Minista
A Turance, IMILI na nufin ‘International Media and Information Literacy Institute’.
Da yake jawabi a Abuja a ranar Talata yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar UNESCO da ta zo duba shirin Nijeriya na kafa cibiyar, Idris ya tabbatar da cewa Nijeriya za ta samu amincewar ƙarshe a taron UNESCO na gaba.
Ya ce: “Tuni mun samu goyon bayan ƙasashe bakwai, kuma akwai ƙasashe kimanin ashirin da suka nuna shirin su na goyon bayan Nijeriya.
“Mun tabbatar da cewa a taron UNESCO na gaba, za a ba Nijeriya damar kafa MIL a Abuja, a Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN).”
Ministan ya bayyana farin cikin sa da sakamako mai kyau da aka samu daga tawagar masu duba shirye-shiryen, kuma ya jaddada cewa Nijeriya ta jajirce wajen cika dukkan sharuɗɗan UNESCO na kafa cibiyar.
Ya ƙara da cewa wannan shirin ba na Nijeriya kaɗai ba ne, har ma da Afrika da sauran duniya baƙi ɗaya.
Ya ce, “Cibiyar Koyar da Ilimin Yaɗa Labarai ba domin al’ummar Nijeriya kawai aka ƙirƙire ta ba, an ƙirƙire ta ne domin al’ummar duniya baki ɗaya.
“Wannan wata dama ce ga ƙasar mu ta nuna ƙwarewa, gogewa, da jajircewa kan Ilimin Yaɗa Labarai na duniya.”
Idris ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da dukkan kuɗaɗen da ake buƙata domin kafa cibiyar, kuma ya ce Ma’aikatar Yaɗa Labarai tana aiki tare da Ma’aikatar Ilimi da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar shirin.
Ya jaddada cewa Koyar da Ilimin Watsa Labarai yana da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da matsalar yaɗa labaran ƙarya wanda ke barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya.
“Yaɗa labaran ƙarya ba matsala ce da ta shafi Nijeriya ita kaɗai ba; matsala ce ta duniya baki ɗaya. Mun yaba da ƙoƙarin da UNESCO ke yi wajen yaƙi da wannan matsalar,” inji Idris.
Da yake kira da a haɗa kai a faɗin duniya domin shawo kan wannan matsalar, ministan ya ƙara da cewa yaƙi da baza labaran ƙarya ba yana nufin tauye ’yancin ’yan jarida ne ba.
Ya ce: “Domin al’umma ta kasance ’yantacciya kuma dimokiraɗiyya ta bunƙasa, ’yancin ’yan jarida yana da matuƙar muhimmanci. Amma domin samun wannan ’yanci, dole ne mu ɗauki nauyin da ke tare da shi. Ba za ka yi amfani da ’yancin ka wajen tauye haƙƙin wani ba.”
A nasa ɓangaren, Mista Nelson Papi Kolliesuah, Babban Manajan Ayyuka na Data-Pop Alliance, wato kamfanin da UNESCO ta ɗauka don tantance shirin da Nijeriya ke yi na kafa cibiyar, ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin ƙasar.
Ya ce sun zo Nijeriya ne domin tabbatar da cewa an cika sharuɗɗan dukkan kayan aiki, ƙarfin aiki, da tsarin gudanarwa da ake buƙata domin kafa cibiyar.
Ya ƙara da cewa sun gamsu da shirye-shiryen da gwamnatin Nijeriya ta yi, inda ya ce cibiyar ta dace da muradun duniya, tsarin ilimi na Nijeriya, da kuma Muradun Cigaba Masu Ɗorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDGs).