• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

by Rabi'u Ali Indabawa
14 hours ago
Duniya

Adadin mutanen da ake zartar wa hukuncin kisa na karuwa a duniya duk da cewa kasashe da yawa sun daina amfani da kisa a matsayin hukuncin manyan laifuka.

A watan Janairun 2024 ne aka yanke wa wani dan Amurka hukuncin kisa ta hanyar amfani da iskar gas, karo na farko da aka yi amfani da irin wannan tsari.

Sannan aka yanke wa wani dan Japan hukuncin kisa saboda wutar da ya cinna wadda ta yi ajalin mutum 36.

  • Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima
  • Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

Wadanne kasashe ne suka daina amfani da hukuncin kisa?

Zuwa karshen 2024, akwai kasashe akalla 145 da suka daina amfani da hukuncin kisa gaba daya a yanzu, idan aka kwatanta da 48 kacal da suka daina ya zuwa shekarar 1991.

LABARAI MASU NASABA

Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

A 2022, kasashe shida ne suka daina yanke hukuncin kisa, ko dai gaba daya ko kuma wani bangare.

Hudu daga cikinsu; Kazakhstan, Papua New Guinea, Saliyo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun jingine shi kwatakwata.

Ekuatorial Guinea da Zambia sun ce za a rika amfani da shi ne kawai kan laifuka mafiya kololuwar muni.

A watan Afrilun 2023, majalisar dokokin Malaysia ta kada kuri’ar daina amfani da shi a matsayin tilas kan laifuka 11, ciki har da kisa da kuma ta’addanci.

Majalisar dokokin Ghana ma ta kada kuri’ar soke hukuncin kisa a watan Yulin 2023.

Wadanne kasashe ne suka fi yanke hukuncin kisa?

Kasashe 20 ne suka zartar da hukunbcin kisa a 2022, idan aka kwatanta da 18 da suka yi hakan a 2021.

Kungiyar kare hakki ta Amnesty International ta ce jimillar mutum 1,518 aka zartar wa hukuncin kisa a duniya, inda aka samu karin kashi 32 cikin 100. Sai dai ta ce hakikanin adadin ya zarta haka sosai saboda yadda kasashe ke boye batun.

Bayan China, Amnesty ta ce kasashen da suka fi kashe mutane a 2024 su ne Iran (972), da Saudiyya (345), da kuma Iraki (63). Su ne suka zartar da kashi 91 cikin 100 na duka kasashen duniya.

Ana yi wa China kallon kasar da ta zarta kowacce aiwatar da hukuncin kisa a duniya, amma ba a sanin hakikanin adadin mutanen, saboda gwamnati ba ta bayyana su.

Kasashen Koriya ta Arewa da Bietnam ma na amfani da hukuncin kisa sosai amma ba su bayyanawa a hukumance.

Amnesty ta ce ta samu rahoton zartar da hukuncin kisa a bainar jama’a akalla sau uku a 2022 a Iran.

Ta ce Iran din ta kashe akalla mutum biyar saboda laifukan da suka aikata a lokacin da suke kasa da shekara 18 da haihuwa.

Saudiyya ta kashe mutane mafiya yawa a duniya a 2022 cikin shekara 30.

Kasashe biyar; Bahrain, Comoros, Laos, Nijar, Koriya ta Kudu – su ne suka yanke wa mutane hukuncin kisa a 2022 bayan sun shafe tsawon lokaci ba su yi amfani da shi ba.

Duk da cewa adadin na raguwa a Amurka, amma ya karu a 2021, amma duk da haka ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da shekarar 1999.

Mutum nawa aka kashe saboda safarar miyagun kwayoyi?

Amnesty International ta ce sama da kashi 40 cikin 100 na mutanen da aka zartar wa hukuncin kisa a 2024 saboda laifukan ta’ammali da miyagun kwayoyi ne.

A 2022, an kashe mutum 325 saboda laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi. Kasashen da suka aikata hakan su ne:Iran 255 Saudiyya – 57 – Singapore – 11

A 2023, Singapore ta zartar da hukuncin kisa kan mace ta farko cikin shekara 20. A 2018 aka kama Saridewi Djaman da laifin safarar hodar ibilis.

Ta yaya kasashe ke zartar da hukuncin kisa?

Saudiyya ce kadai ta zayyana fille kai a matsayin hanyar aiwatar da hukuncin kisa a 2022.

Sauran hanyoyin sun hada da rataya, da allura mai guba, da kuma harbi da bindiga.

A watan Janairun 2024 jihar Alabama ta Amurka ta zartar wa wani mai laifin kisa Kenneth Smith hukuncin kisa ta hanyar amfani da iskar nitrogen gas.

Ya zama mutum na farko a duniya da aka zartar wa hukuncin ta irin wannan hanyar, a cewar cibiyar Death Penalty Information Center da ke Amurka.

Lauyoyin Mista Smiths sun ce salon da ba a taba gwadawa ba kafinsa “rashin imani ne”.

Alabama da wasu jihohin Amurka biyu ne suka amince da amfani da iskar gas din saboda kwayoyin da ake amfani da su wajen yi wa mutum allura mai guba ba sa samuwa cikin sauki.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kano
Manyan Labarai

Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi

November 3, 2025
Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
Manyan Labarai

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Next Post
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.