• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙoƙarin Ƙungiyoyin Afrika A Gasar Kofin Duniya

by Abba Ibrahim Wada
4 months ago
afrika

Gasar cin Kofin Duniya ta kungiyoyi ko kuma FIFA Club World Cup da a yanzu ake gudanarwa a kasar Amurka za ta bai wa tawagogin Afirka hudu da za su buga gasar karin damar bajakolin ‘yan wasan Afirka da kuma irin yadda kasashen na Afirka suke kokarin ganin sun fara goga kafada da kafada da manyan kungiyoyi a nahiyar Turai da kuma kudancin Amurka.

Kungiyar Al Ahly ta Masar da ta lashe kofin Champions League na Afirka sau 12, da Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu, da Wydad Casablanca ta Morocco, da Esperance ta Tunisia, su ne za su nemi murkushe takwarorinsu na Turai da sauran nahiyoyin duniya da a yanzu suke fafatawa a gasar da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta shirya a karon farko.

  • Su Waye ‘Yan Afirka Da Suka Canja Kungiya A Turai?
  • Anya Nahiyar Afirka Fili Ne Na Gudanar Da Takara?

Babu wata kungiya daga Afirka da ta taba lashe kofin gasar ta Club World Cup a tarihi, inda biyu ne kawai suka taba kai wa wasan karshe a karo 20 na gasar. Amma yanzu akwai ladan da za a samu – jimillar abin da za a bayar ya kai Dala biliyan daya, inda aka ware Dala miliyan 475 don bai wa wadanda suka fi kokari. Duk da cewa FIFA ta kara yawan wasannin da aka saba bugawa duk da yawan wasannin da ke gaban kungiyoyi, kocin Esperance Maher Kanzari ya ce “dama ce” ga ‘yanwasa su bayyana kansu.

Duka kungiyoyin Afirka da za su buga gasar ta Kofin Duniya za su samu ladan akalla Dala miliyan 9.55 – irin wadannan wakilai daga Asiya da Arewacin Amurka da Amurka ta Tsakiya za su samu. Wannan adadi ya ninka Dala miliyan hudu da Palmiras ta samu bayan lashe kofin zakarun nahiyar Afirka.

Duk da haka, ladan da kungiyoyin Afirka za su samu shi ne mafi kankanta. Wakilan Kudancin Amurka shida za su samu ladan Dala miliyan 15.21, yayin da kungiyoyin Turai 12 za su samu kudi daga Dala miliyan 12.81 zuwa 38.19.

LABARAI MASU NASABA

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

Nasarar da kungiya ta samu a matakin rukuni za a ba ta Dala miliyan biyu, canjaras kuma miliyan daya, wadda ta cinye kofin kuma za ta samu ladan Dala miliyan 40. Ganin yadda kungiyoyin Turai suka mamaye gasar, Afirka na fatan samun karin dama a nan gaba, ma’ana a Karara nahiyar Afirka yawan kungiyoyin da za su dinga wakiltar ta.

Wasu na fatan kungiyoyin Afirka da ke cikin gasar za su ja hankalin duniya zuwa nahiyar ko da kuwa gasarta ta zakaru ba ta iya yin hakan ba, da kuma kawo musu kudi idan aka kwatanta da takwarorinsu.

Sabuwar gasar African Footbal League da hukumar CAF ta kaddamar a 2023 ba a sake yin ta ba, duk da irin rigingimun da aka yi lokacin da aka fara ta, mai tawaga hudu wadda kungiyar Sundowns ta lashe.

Kungiyar Pretoria da shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF, Patrice Motsepe ya mallaka, ta kafa kanta a matsayin jagora a harkar kwallon kafar Afirka – ita ta lashe kofunan gasar Afirka ta Kudu tara na baya-bayan nan.

Sundowns za su kara da Ulsan HD da Borussia Dortmund da Fluminense a Rukunin F, abin da wani magoyi kwallon kafa ya ce zai taimaka wajen nasararta a gasar ta Club World Cup.

Lokacin gudanar da gasar Club World Cup ya shafi harkokin wasa a Afirka, ta yadda sai da aka matsar da lokacin gudanar da gasar Kofin kasashen Afirka wato AFCON 2025 daga watannin Yuni da Yuli zuwa karshen shekarar ta 2025. Tuni kungiyar kwararrun ‘yankwallo ta duniya ta shigar da kara a shekarar da ta gabata kan abin da suka kira “nuna karfin iko” da FIFA ta yi wajen fadada gasar, amma kuma duk da haka ba a dakata ba.

Danwasan Nijeriya na AC Milan Samuel Chikwueze ya ce kungiyarsa ba za ta buga gasar ba, amma duk da haka yawan wasannin da za su buga sun yi yawa. ‘Yan wasan dai sun yi korafin cewa lokaci daya da ‘yanwasa za su huta shi ne daidai lokacin da suka saka gasar. ‘Yan wasan sun bayyana cewa abu ne mai wahala buga wasanni masu yawa domin mutum zai gajiyar da kafufuwansa da tunaninsa ta yadda ma ba zai ji dadin buga wasan ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya
Wasanni

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

October 19, 2025
Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya
Wasanni

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

October 18, 2025
Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba
Wasanni

Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

October 18, 2025
Next Post
Rasuwar Ɗantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya –  Shugaban ƘasaTinubu

Rasuwar Ɗantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya -  Shugaban ƘasaTinubu

LABARAI MASU NASABA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

October 19, 2025
Yadda Ake Alkaki

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.