Tun daga ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, lokacin da majalisar wakilai ta bayyana karbar shawarwarin kudirin samar da sabbin jihohi 31 a Nijeriya a wani yunkuri na ci gaba da sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar na 1999, ya raba kan ‘yan Nijeriya a halin yanzu.
kudirin samar da sabbin jihohin idan aka samar da su, za su kara yawan jihohin Nijeriya daga 36 zuwa 67. A halin yanzu, Nijeriya na da jihohi 36, yankin kudu maso gabas na da jihohi biyar. Kudu maso yamma da kudu maso kudu da arewa ta tsakiya da arewa maso gabas suna da jihohi shida kowacce, yayin da arewa maso yamma ke da jihohi bakwai.
- Ɗalibin Jami’a Ya Hallaka Kansa Saboda Matsin Rayuwa A Jihar Kwara
- Wani Jami’in Ɗansanda Ya Bindige Kansa Har Lahira A Jihar Nasarawa
A cewar kudirin, yankin arewa ta tsakiya ta samu bukatu na samar da jihohi bakwai da suka hada da jihohin Benue Ala, Apa Agba, da Apa daga Jihar Benuwai ta yanzu; Jihohin Okun, Okura da Confluence daga Jihar Kogi ta yanzu, da kuma daukaka babban birnin tarayya Abuja zuwa matsayin jiha.
Har ila yau, a yankin arewa maso gabas, akwai shawarwarin samar da jihohin Amana, Katagum Sabannah da Muri daga jihohin Adamawa, Bauchi, Borno da Taraba na yanzu, bi da bi. Haka nan, akwai shawarwarin samar da sabbin jihohi biyar, wato New Kaduna da Gurrara, daga Jihar Kaduna ta yanzu; Jihohin Tiga da Ghari, daga Jihar Kano ta yanzu da kuma Kainji daga Jihar Kebbi.
A kudu maso gabas, jihohin da ake son kirkira sun hada da Etiti da za a samar daga jihohi biyar da ake da su a shiyyar; Adada daga Jihar Inugu, Orashi, Orlu da Aba da za a kirkiro daga jihohin Imo da Abiya.
Sannan a kudu maso kudu, masu goyon bayan sabbin jihohi suna son a samar da jihohin Ogoja, Warri, da Bori daga jihohin Kuros Ribas, Delta da Ribas, da kuma Jihar Obolo daga jihohin Ribers da Akwa Ibom na yanzu.
Daga kudu maso yamma kuwa, akwai shawarwarin samar da sabbin jihohi shida. Jihohin da ake shirin kirkira sun hada da Toru-ebe da za a sassaka daga jihohin Delta da Edo da Ondo na yanzu, da kuma jihohin Ibadan da Lagoon da za a sassaka daga jihohin Oyo da Legas, bi da bi. Sauran sun hada da Jihar Ijebu da za a samar daga Jihar Ogun ta yanzu da kuma jihohin Oke-Ogun da Ife-Ijesha da za a kirkiro daga jihohin Ogu da Oyo da Osun na yanzu.
Kwamitin majalisar kan sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar nan, a wata sanarwa da ya aike wa mambobin majalisar wakilai, mai dauke da sa hannun mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin, ya umurci masu goyon bayan kirkiro sabbin jihohin da su sake gabatar da bukatarsu kamar yadda sashe na 8 (1) na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada.
“Kwamitin ya duba shawarwarin samar da sabbin jihohi kamar yadda sashe na 8(1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 ya tanada. Wannan sashe ya zayyana takamaiman bukatu wadanda dole ne a cika su don fara aikin kirkirar sabbin jihohi. Za a sake gabatar da shawarwari bisa la’akari da wadannan sharudda,” in ji Kalu.
Wasu ‘yan Nijeriya dai sun soki matakin, suna masu cewa abin da ya kamata shugabanni su mayar da hankali a kai shi ne, yadda za a mayar da kasar mulkin yanki ba wai samar da karin jihohi ba.
Masu yada wannan labari na ganin cewa Nijeriya ta fi samun shugabanci nagari a lokacin da ake tsarin milkin yankuna, lura da cewa samar da jihohi 12 daga yankuna hudu da gwamnatin mulkin soja ta Janar Yakubu Gowon ta yi ba don wani ci gaba ba ne, sai dai wani yunkuri ne na raunana yankin gabas a lokacin yakin Biafara.
Amma, akwai wadanda kuma suka yi jayayya cewa samar da jihohi yana kawo ci gaba ga mutanen da ke ganin an ware su kuma za su yi maraba da shawarwarin muddin sun bi ka’idojin kamar yadda ‘yan majalisar suka sake nanata a baya.
Haka kuma, akwai wasu da ba su yarda da samar da karin jihohi a Nijeriya gaba daya ba, amma suna da ra’ayin cewa a yi adalci a kara wa yankin kudu maso gabas karin jiha daya domin daidaita yankin da takwarorinsa.
kungiyoyin yankin biyu da suka yi kaurin suna wajen nuna adawa da matakin sun hada da kungiyar kabilar Yarbawa ta Afenifere da kuma kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF). Dukkan bangarorin biyu sun bayyana shirin samar da jihar a matsayin abin dariya kuma ba amshesshe ba ne.
Sai dai kungiyar ta Afenifere ta bukaci majalisar dokokin kasar da ta mayar da hankali kan sauye-sauyen kundin tsarin mulkin kasar da zai raba madafun iko, da maido da albarkatun kasa a yankunan, da kuma bai wa jihohi ‘yancin cin gashin kansu domin su bunkasa cikin hanzari.
Haka zalika, kungiyar tuntuba ta Arewa, ta kuma bayyana rashin amincewarta da shirin samar da sabbin jihohi 31, inda ta bayyana ra’ayin a matsayin wanda bai kamata ba.
Amma, babbar kungiyar kare al’adun Igbo, Ohanaeze Ndigbo ta bi wata hanya ta daban. Tana da ra’ayin cewa a kara wa yankin kudu maso gabas sabbin jihohi domin magance kura-kuran da aka yi wa yankin dangane da batun samar da jihohi.
A nasa bangaren, Babban Lauyan Nijeriya kuma Farfesa a fannin shari’a, Cif Mike Ozekhome, ya bayyana hakan a matsayin almubazzaranci.
Shima da yake magana game da damuwar da ‘yan Nijeriya da dama ke da shi dangane da yadda ake tada zaune tsaye na samar da sabbin jihohi, Mista Osita Okechukwu, tsohon Darakta Janar na Muryar Nijeriya ya yaba da matakin a matsayin kyakkyawan misali ga hadin kan kasa.
Najeeb Bello ya kasa boye bacin ransa game da lmarin, inda ya ce, “Me zai hana smar da jihohi 311? A bari kowace karamar hukuma a Nijeriya ta zama jiha kawai.”
Bashir Ahmad yana goyan bayan samar da sabbin jihohi, amma ya bayar da shawara a kara karkasa Jihar Kano duba da yawan al’ummar da take da shi.