Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi fatali da karin farashin man fetur zuwa N617, inda ta ce wannan lamari sam bai wa ‘yan Nijeriya dadi ba.
Da yake mayar da martani game da karin farashin, babban jami’in yada labarai da harkokin jama’a na kungiyar, Kwamared Benson Upah, ya shaida wa LEADERSHIP cewa, karin farashin babbar barazana ce ga rayuwar ‘yan kasa da tattalin arzikinsu da sana’o’insu.
NLC ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba matakanta na kudirin kai farashin man fetur zuwa Naira 1,000 ga kowace lita.
Ya ce, har yanzun kungiyar ba ta gamsu da cewa, cire tallafin man fetur din zai amfanar da jama’a ko tattalin arzikin kasa ba ko kuma cewa, cire tallafin zai sake karfafa guiwar ‘yankasa kan samun sabuwar rayuwa mai inganci.
“Muna ba gwamnati shawara da ta ja da baya daga wannan tafiya, jama’a ba su ji dadin hakan ba, bai kamata a dauki hakurin ‘yan kasa a wulakance ba,” inji shi.