Farashin Litar Man Fetur ya karu zuwa Naira 617 kamar yadda rahotanni suka bayyana a babban birnin tarayya, Abuja.
Gidajen man NNPC da ke Abuja sun daga farashin man daga Naira 539 zuwa Naira 617 kan kowace lita.
- Lauyoyi 60 Sun Yi Karar DSS Kan Kin Sakin Emefiele
- Gwamna Zulum Ya Raba Tallafin Kayan Abinci Ga Magidanta 13,000 A Gwoza
Ya zuwa yanzu dai ba a san dalilin da ya sa aka yi karin farashin man fetur din ba.
Talla
Amma ba zai rasa nasaba da batun da ‘yan kasuwar man fetur din suka yi na cewa farashin na iya kai wa Naira 700 kan kowace lita a baya.
Amma har yanzu Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NDMPRA), ba ta ce uffan kan rahoton karin man fetur din da Jaridar Daily Trust ta yi ba.
Bayani na tafe…
Talla