Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta kasa (MACBAN) ta nuna nuna damuwarta dangane rashin sanin halin da mataimakin shugaban kungiyar na kasa, Injiniya Mannir Atiku Lamido, tsawon shekaru biyu babu labarinsa.
A wani taron manema labarai a Kaduna, wanda sakataren kungiyar Alhaji Bello Aliyu Gotomo, ya yi ya bayyana rashin gamsuwarsu da irin matakin da jami’an tsaro suke dauka wajen gano halin da mataimakin shugaban nasu yake ciki duk da cewa suna ikirarin yin bakin kokarinsu.
- Lokaci Ya Yi Da Za A Kawo Karshen Musguna Wa Fulani – Dakta Awwal
- Kungiyar Fulani Ta MACBAN Ta Nesanta Kanta Daga Zanga-zangar Matasa
Haka zalika, ya bayyana danuwarsu dangane da yadda matsalar rashin tsaro take kara ta’azzara a jihohin Arewacin kasar nan, musamman jihohin Adamawa da Borno da Nija da Katsina da dai sauransu, inda ya ce akwai bukatar hukumomin tsaro su kara zage damtse wajen kawo saukin lamarin.
Ya ci gaba da cewa, “Jami’an tsaro sun shaida mana cewa suna bakin kokarinsu wajen gano halin da Injiya Manir Atiku yake ciki, amma abin da ya ba mu tsoro da shakku shi ne, sun ce sun yi kokarin bibiyar lambar wayarsa domin gano inda yake amma abin da bai yiwuba saboda a cewarsu, an goge komai a wayarsa wanda babu wata hanya da za a iya gano inda yake ta hanyar bibiyar wayarsa. Sun ce a yanzu babu wani bayani da za a iya samu dangane da batar nasa.
“Muna kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su taimaka mana su gano halin da dan uwanmu yake ciki, yau shekaru biyu kenan babu labarinsa.”
Mataimakin shugaban kungiyar MACBAN ta kasa ya bace ne a ranar 20 ga watan Yuni na shekarar 2023 a garin Zariya, inda aka tsinci motarsa a bakin hanya a bude, lamarin da haifar da fargaba da jimami, wanda har yanzu babu wani bayani dangane da halin da yake ciki.
Sai dai sakataran ya bayyana jin dadinsu bisa samar da ma’aikatar bunkasa harkokin Fulani da Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp