Ƙungiyar Sadarwa ta Ƙasa (National Communication Team) ta kammala taron duba yadda ta gudanar da ayyukan ta a tsakiyar wa’adin ta, tare da ɗaukar sababbin matakai na ƙara bayyana nasarorin da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke samu.
Ƙungiyar ta ƙunshi hukumomi da jami’ai na Gwamnatin Tarayya waɗanda alhakin shelar ayyukan gwamnatin Tinubu ya rataya a wuyan su.
- Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo
- Noman 2025: Dole Ne Manoma Su Kiyaye Hasashen Hukumar NiMet
Taron ya gudana ne a Abuja ƙarƙashin jagorancin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, a ranar Juma’a.
A sanarwar da mataimaki na musamman ga ministan kan harkar yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim ya fitar, ya bayyana cewa a jawabin sa na buɗe taron, ministan ya nuna jin daɗin sa kan yadda haɗin kai ke ƙaruwa a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki a fannin yaɗa labarai a cikin gwamnatin.
Ya ce haɗin kan da daidaiton manufa sun ƙara inganta isar da saƙo da kuma fahimtar manufofin gwamnatin Tinubu.
Ministan ya yaba da yadda Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take aiki tare da shugabannin hukumomin yaɗa labarai da kuma mataimakan shugaban ƙasa a ɓangaren watsa labarai da dabarun sadarwa.
Ya ce wannan haɗin gwiwa ya taimaka wajen tabbatar da cewa saƙonnin gwamnati suna da tsari, suna dogara da hujjoji, kuma suna amsa buƙatun jama’a.
Ya jaddada cewa wannan haɗin gwiwa ya taimaka wajen gina amincewar jama’a da kuma ƙara wayar da su game da tasirin Ajandar Sabunta Fata a ɓangarori masu muhimmanci kamar tattalin arziki, ababen more rayuwa, lafiya, ilimi da ayyukan jinƙai.
Ministan ya buƙaci masu ruwa da tsaki da su ci gaba da haɗa kai, tare da tabbatar da aiki cikin ƙwarewa, domin ƙara ƙarfafa wayar da jama’a kan nasarorin gwamnati a cikin gida da waje.
Ƙungiyar ta cimma matsaya kan a ƙara mayar da hankali wajen nuna nasarori a fannonin raya karkara, noma, gine-ginen ababen more rayuwa da kuma yaƙi da rashin tsaro, waɗanda su ne suka shafi rayuwar al’umma kai-tsaye.
Don ƙarfafa wannan yunƙuri, Idris ya buƙaci da a ci gaba da gudanar da tarurrukan tuntuɓa a jihohi da Babban Birnin Tarayya.
Ya ce tarurrukan tuntuɓar za su ba da damar tattaunawa kai-tsaye tsakanin wakilan gwamnati da jama’a, wanda hakan zai taimaka wajen gina amincewa, gaskiya da kuma gwamnatin da jama’a ke da tasiri a cikin ta.
Ƙungiyar ta bayyana aniyar ta ta ci gaba da yaɗa bayanai da za su ƙarfafa tattaunawar ƙasa, domin nuna tasirin ƙoƙarin gwamnati da kuma ƙarfafa haɗin kai da shiga cikin harkokin mulki.
Taron ya samu halartar shugabannin hukumomin yaɗa labarai da suka haɗa da Darakta Janar na NTA, Kwamared Abdulhamid Dembos; Darakta Janar na FRCN, Dakta Mohammed Bulama; Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), Malam Lanre Issa-Onilu; Darakta Janar na VON, Malam Jibrin Baba Ndace; Darakta Janar na ARCON, Dakta Olalekan Fadolapo; da Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Jaridu ta Ƙasa, Dakta Dili Ezegha.
Sauran su ne Manajan Darakta na NAN, Malam Ali M. Ali; Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Mista Bayo Onanuga; Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Mista Sunday Dare; da Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Dabarun Bayanai, Mista Daniel Bwala.
Haka zalika, akwai masu taimaka wa Shugaban Ƙasa da suka haɗa da Tope Ajayi (kan Harkokin Labarai), Abdulaziz Abdulaziz (kan Jaridu), Mista Otega Ogra (kan Sadarwar Zamani), Linda Akhigbe (kan Sadarwa ta Dabaru), da kuma Ali Audu (kan Harkokin Jama’a).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp