Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai mummunan hari a ofishin ƴansanda na garin Zonkwa a ƙaramar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna, inda suka kashe a ƙalla jami’an jami’ai biyu da ke bakin aiki.
Harin, wanda ya auku da yammacin Juma’a, ya jefa mazauna garin cikin tsoro da tashin hankali, domin ba su taba tsammanin cewa za a kai irin wannan hari kai tsaye kan ofishin jami’an tsaro ba.
- Yadda Ƴan Agbero’ Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Abuja
- Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe
Wani ganau da ke kusa da wurin ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun zo ofishin ƴansandan ne ɗauke da makamai, suka buɗe wuta babu kakkautawa domin tsoratar da jama’a da maƙwabta na wurin. Ya ce manufarsu ita ce su kuɓutar da wasu da ake zargi da an kawo su ofishin ƴansandan daga garin Kachia. “Sai daga baya suka gane cewa waɗanda suke nema ba a tsare da su a Zonkwa,” in ji wani jami’in tsaro da ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴansanda ta jihar Kaduna, DSP Hassan Munsir, bai yi nasara ba a lokacin da ake haɗa wannan rahoto, haka kuma ba a samu sunayen jami’an da suka rasu ba. Har yanzu babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar Kaduna ko na ƙaramar hukumar Zangon Kataf dangane da lamarin har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.