Rundunar Ƴansandan jihar Kwara ta tabbatar da mutuwar dagacin ƙauyen Ogbayo da jami’an tsaro ƴan sa-kai 11 bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai a Oke-Ode, ƙaramar hukumar Ifelodun, jihar.
Mai magana da yawun rundunar, Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, inda maharan suka shiga ƙauyen suna harbi ba ƙaƙƙautawa. Ta ƙara da cewa an kai gawarwakin waɗanda suka mutu asibiti, yayin da wasu mutum huɗu da suka samu raunuka daga harbin bindiga ke karɓar magani.
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Da Gonaki A Kogi, Ta Tsaida Aiyuka A Legas
- ’Yansanda Sun Kama ‘Yan Fashi A Kaduna, Sun Ƙwato Bindiga Da Wayoyi
Ta ce jami’an tsaro sun haɗa kai da Sojoji da kuma jami’an tsaron dazuka wajen gudanar da sumame domin cafke waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki. Rundunar ta kuma tabbatar da cewa ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen zaƙulo maharan tare da gurfanar da su a gaban doka.
Kwamishinan ƴansanda na jihar, CP Adekimi Ojo, ya yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu tare da yi musu addu’ar samun rahama. Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar Kwara cewa rundunar ƴansanda za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp