Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), ta ce ‘yan bindiga sun kashe mata limaman choci 23 a jihar Kaduna.
Can ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta fitar, ta cikin shekaru hudu sun rufe kimanin mujami’u 200 da ke faɗin jihar Kaduna sakamakon hare-haren ‘Yan bindigar.
Shugaban CAN na kasa reshen jihar Kaduna, Rev. John Hayab, ya bayyana damuwarsu kan yadda lamarin ya yi kamari sosai.