Wani rahoto da kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited ya fitar ya bayyana cewa mutum 1,111 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 276 aka yi garkuwa da su a faɗin Nijeriya cikin watan Yuni 2025, sakamakon hare-haren ƴan bindiga da wasu ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba.
Rahoton ya nuna cewa an samu raguwar hare-haren tsaro idan aka kwatanta da watan Mayu 2025, inda aka samu saukar kashi 48.04% na adadin hare-haren daga 895 zuwa 465. Haka zalika, mace-mace sun ragu da kashi 14.27%, daga mutum 1,296 a watan Mayu zuwa 1,111 a Yuni. Garkuwa da mutane ma ta ragu sosai da kashi 74.59%, daga 1,086 zuwa 276.
- An Tsaurara Matakan Tsaro A Daura Gabanin Jana’izar Buhari A Gobe Talata
- Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe
A cewar rahoton, mafi yawan mace-macen sun faru ne a tsakanin fararen hula da suka kai kashi 72.37% na dukkan waɗanda suka mutu. Rikicin manoma da makiyaya a yankin Arewa ta tsakiya na daga cikin manyan dalilan mace-mace, yayin da Arewa maso Yamma ta fi yawan sace mutane da kashi 72.10% na adadin waɗanda aka yi garkuwa da su.
A nazarin watanni uku na ƙarshe, an gano cewa rikice-rikice sun ragu da kashi 1.95%, amma mace-mace sun ƙaru da kashi 5.66%, inda Arewa ta tsakiya ta fi yawan hauhawar tashe-tashen hankula. Jimillar mutane 6,800 ne suka mutu a rabin shekarar farko ta 2025, ƙarin kashi 19.11% idan aka kwatanta da rabin shekarar farko ta 2024.
Jihar Zamfara ce ta fi kowacce jiha yawan mace-mace da 1,088 tare da fiye da 1,755 da aka yi garkuwa da su. Rahoton ya nuna cewa yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas na ci gaba da fuskantar barazanar ƴan ta’adda, yayin da Arewa ta Tsakiya ke fama da rikicin makiyaya da manoma da kuma hare-hare a jihohin Neja, Binuwe, Filato da Kwara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp