A ƙalla mutane 14 ne aka sace yayin da wasu ƴan bindiga suka kai hari a ƙauyen tsohuwar tasha dake unguwar Ruwan Doruwa a ƙaramar hukumar Maru, jihar Zamfara.
Media smarts News ta rawaito cewa, harin ya faru da misalin ƙarfe 3:45 na safe ranar Lahadi, inda ƴan bindigar suka mamaye ƙauyen, suka tafi da mata 11 da yara uku. Haka kuma, suka kashe wani mazaunin garin, mai suna Alhaji Rabe, wanda ya yi ƙoƙarin tare masu hanya.
- A Zamanantar Da Tsarin Karatu A Makarantun Koyar Da Ilimin Addinin Musulunci – ECOWAS
- NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama
Mai garin ƙauyen, Alhaji Mahmud Bello, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce harin ya faru ne yayin da mazauna ƙauyen ke barci. “Sun ƙarya kofofin gidajenmu ta ƙarfi, ba mu da makamai don mu kare kanmu. Ta doke suka sa kawai suka sa muka kwanta ƙasa ba tare da wani motsi ba, yayinda matanmu ke ihun neman taimako,” in ji shi.
Wani mazaunin garin, Alhaji Usman Ali, wanda ya shaida mutuwar Alhaji Rabe, ya bayyana yadda lamarin ya kasance. “Na ji yana faɗa wa matansa kada su bi ƴan bindigar, su gudu. Sai kawai muka ji harbin bindiga, hankali ya tashi, ban sake jin muryarsa ba,” ya bayyana.
Haka kuma, wani mazaunin ƙauyen, Yakubu Dogo, ya bayyana harin a matsayin mafi muni da ƙauyen ya taɓa fuskanta. “Sun taɓa kai harin sau biyu a wannan ƙauye da sau biyu a Masama, amma ba su taɓa kashe ko sace kowa ba. Abin da ya faru daren jiya abin takaici ne kuma mai tayar da hankali,” in ji shi.
A halin yanzu, masu sa ido na ƙauyen tare da wata tawagar tsaro ta haɗin gwuiwa daga tsohuwar tasha da Ruwan Doruwa sun fara aikin neman wadanda har yanzu ba a samu ba.














