Yan bindiga sun sace Tasiu Habibu, Shugaban ƙungiyar Direbobin Motoci ta ƙasa (NURTW) a garin Kidandan, ƙaramar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.
Ƴan bindigar sun kuma sace yara uku yayan wani ma’aikacin lafiya a garin yayin da suka kai harin da da misalin ƙarfe 9:30 na daren jiya ranar Asabar.
- Mun Samu ‘Yan Takara Masu Tu’ammali Da Miyagun Kwayoyi – Hukumar Zaben Kaduna
- Gwamna Sani Ya Sasanta Rigingimun Filaye 347 A Kaduna
‘Yan bindigar sun yi amfani da ruwan saman da ake yi kamar da bakin kwarya wanda ya sa yawancin mutanen ƙauyen sun shige gidajensu, inda suka sace su ba tare da wani kalubale ba. Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun zo cikin shiri suna harbi domin tsorata mutanen garin.
Tasiu Habibu an taɓa yin garkuwa da shi a baya, inda aka riƙe shi na tsawon kwanaki 60 kafin a sake shi bayan biyan kuɗin fansa. A wannan sabon harin, wani ɗan ƙauyen da ake kira Idris Jibril ya samu raunin harbe amma an garzaya da shi asibiti don samun kulawa.
Har yanzu ba a sami wani jawabi ba daga ‘Yansandan Jihar Kaduna kawo lokacin hada wannan rahoton.