Rundunar ƴansanda ta jihar Kwara ta daƙile yunƙurin sace mutane biyu tare da cafke mutum huɗu da ake zargi da hannu a lamarin a ƙananan hukumomin Ifelodun da Baruten.
Kakakin rundunar, Toun Ejire-Adeyemi, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke su ne bayan bin diddigin kiran wayar barazana da wasu mutane suka samu a Ifelodun da Ilesha-Baruba, inda aka buƙace su biya kuɗin fansa har Naira miliyan tara.
- Yadda Ficewar Kwararrun Ma’aikata Daga Nijeriya Ke Barazana Ga Tattalin Arzikin Kasa
- Ɗalibin Jami’a Ya Hallaka Kansa Saboda Matsin Rayuwa A Jihar Kwara
Bincike ya kai ga cafke Umar Sanni daga jihar Neja da Dairu Isiaku daga Ifelodun, da kuma Tukur Muhammad da Yahaya Abdullahi, waɗanda suka amsa laifin yin barazana da ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa. An gurfanar da su a kotu, kuma an tura su gidan yari domin ci gaba da shair’a.