A wani mummunan al’amari da ya faru a yau, an tabbatar da mutuwar jami’an Ƴansanda biyu, yayin da wasu uku suka samu raunuka a wani hari da ‘yan Shi’a, suka kai kan Ƴansandan a Abuja yau Lahadi.
An ruwaito dai cewa harin ya faru ne ba tare da wani dalili ba a wani shingen bincike na Ƴansanda a Wuse, inda ake zargin ƴan ƙungiyar sun yi amfani da wuƙa, da Adda da wasu ababen fashewa.
- Gyaran Gashi Ya Yi Kyau Da Laushi
- NDLEA Ta Cafke Wani Ɗan Kasuwa Ya Haɗiye Hodar Iblis Ƙulli 88 A Abuja
Mai magana da yawun rundunar Ƴansandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an ƙona motoci guda uku na sintirin Ƴansanda yayin rikicin.
“Rundunar Ƴansandan Abuja tana tabbatar da harin da aka kai ba tare da wani dalili ba daga ƙungiyar IMN, wato ‘yan Shi’a, kan jami’an Ƴansanda a Wuse Junction. Harin ya yi sanadiyyar mutuwar jami’ai biyu, uku sun raunata, sannan an lalata dukiyoyi da dama,” inji ta.
Kwamishinan Ƴansanda na Abuja, CP Benneth Igweh, ya yi Allah-wadai da harin, tare da tabbatar da cewa za a hukunta duk masu hannu a lamarin.
An riga an kama wasu mutane yayin da bincike ke ci gaba. Ƴansanda sun tabbatar da dawo da zaman lafiya a yankin, kuma suna ci gaba da sanya ido kan yanayin.