Rundunar ƴansanda ta jihar Kano ta sanar da ƙaddamar da wani sabon shiri mai suna “Operation Kukan Kura”, wanda aka ƙirƙira domin yaƙi da ayyukan ta’addanci da aikata laifuka a faɗin jihar. Wannan mataki ya kai ga kama mutum 98 cikin gajeren lokaci.
Kwamishinan ƴansanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a shalƙwatar rundunar da ke Bompai, inda ya ce sabon shirin zai mayar da hankali kan yaƙi da daba, fashi da makami, satar mutane, da safarar miyagun ƙwayoyi.
- Namadi Sambo Ya Yaba Wa Gwamna Abba Yusuf Kan Bunƙasa Ɓangaren Ilimi Da Gine-Gine A Kano
- Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen Shugabancin Jami’ar Bayero Ta Kano
A cewar Bakori, shirin ya ƙunshi dabarun bincike na zamani, ayyukan sintiri da farmaki a wuraren da ake zargi da zama mafakar masu laifi. Ya bayyana cewa wadanda aka kama suna da hannu a manyan laifuka da suka addabi birnin Kano da kewaye.
Kwamishinan ya kara da cewa rundunar zata ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da yin kira ga jama’a da su rika bayar da bayanai da goyon baya domin samun nasara a wannan aiki.
A karshe, Bakori ya bukaci hadin kan shugabannin al’umma, matasa da kungiyoyin farar hula wajen tallafa wa jami’an tsaro da bayanai masu amfani don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp