Rundunar ƴansanda ta ƙasa (NPF) a Zone 1 ta Kano ta tabbatar da cewa tana gudanar da bincike kan wani ɗan jarida kuma mai gabatar da shirye-shirye ta yanar gizo, Ibrahim Ishaq, wanda aka fi sani da Ɗan Uwa Rano, bisa zargin ɓata suna.
Tabbatarwar ta fito ne bayan zaman zullumi da damuwar da jama’a suka shiga kan tsare ɗan jaridar da aka yi a ranar Asabar, wanda ake zargin ya samo asali ne daga ƙorafin da Abdullahi Rogo, Darakta Janar na hulɗa a fadar gwamnatin Kano, ya shigar. Rahotanni sun ce Rogo yana cikin binciken EFCC da ICPC kan zargin sama da faɗi da kuɗaɗe na kusan Naira biliyan 6.5.
- Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano
- Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta
Wasu daga cikin abokan aikin Ishaq sun shaida cewa an kama shi ne ba tare da nuna takardar kame ba, a lokacin da yake aiki a ofishinsa a Kano, sannan aka garzaya da shi zuwa ofishin ƴansanda na Zone 1 don amsa tambayoyi kan wani sharhi da ya yi a cikin shirin sa na “Imalu” da yake yaɗawa ta kafar yanar gizo.
Sai dai a wata sanarwa da Jami’in hulda da jama’a na shirya ta ɗaya, CSP Bashir Muhammad, ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa AIG Ahmed Garba ne ya bayar da umarnin a gayyaci ɗan jaridar domin bincike bisa ƙorafin da aka samu kansa.
Sanarwar ta ce, “Bayan kammala cikakken bincike, idan aka same shi da laifi, za a gurfanar da shi a kotu.”
Ƴansandan sun kuma yi kira ga ƴan jarida da su tabbatar da daidaito a rahotanninsu, tare da tuntuɓar sashin hulɗa da jama’a na yankin kafin yaɗa labaran da ke da sarƙakiya. AIG Garba ya gargaɗi ƴan jarida da su guji tsoma baki a cikin binciken da ke gudana, yana mai cewa “a bar doka ta yi aikinta.”
Sai dai sanarwar ba ta fayyace halaccin tsarewar farko da aka yi wa ɗan jaridar ba, ko kuma ko an kama shi ne ba tare da takardar izinin kame ba.
A halin yanzu, ƙungiyoyin kare ƴancin ƴan jarida da ƙungiyoyin farar hula da dama suna ci gaba da kira ga ƴansanda da su saki Ishaq tare da dakatar da duk wani yunƙuri na tsoratar da ƴan jarida daga gudanar da aikinsu cikin ƴanci.