Rundunar Ƴansanda babban birnin tarayya (FCT) ta kama mutane uku da ake zargi da kisan Mr. Azubuko Nwakama, Ɗan jarida mai aiki da Liberty Radio, wanda aka kashe a kasuwar Panteka, Mpape, Abuja, a ranar 14 ga Yuni, 2024. Masu laifin sun yi masa fashi da sace wayarsa da wasu kayayyaki kafin su tsere.
Bayan faruwar lamarin, Ƴansanda sun fara bincike, amma sun kasa gano wayar duk da ƙoƙarin bin sawunta. Nasarar ta samu ne a ranar 2 ga Agusta, 2025, lokacin da aka kunna wayar, Redmi 13C, aka gano tana hannun Mutari Lawal mai shekaru 32 daga jihar Kano. Ya amsa cewa shi ne ya kai wa mamacin hari tare da caka masa wuka kafin ya sace kayayyakin.
- NDLEA Ta Cafke Masu Baburan Da Ke Kai Saƙon Muggan Ƙwayoyi A Abuja
- UADD Ta Yaba Wa Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Kan Himma Da Kishin Kasa
Mutari ya bayyana sunayen abokan aikinsa a masu suna Ɗan Asabe Ibrahim, mai shekaru 22 daga Zamfara, da Danjuma Ibrahim, mai shekaru 18, waɗanda ba su da adireshin dindindin a Mpape. Ya ce ya kai wayar Kano, ya ajiye ta a kashe tsawon shekara guda, sannan ya kunna ta a watan Agusta 2025 domin goge bayanai da saka katin SIM dinsa kafin ya dawo Abuja.
Kwamishinan Ƴansanda na FCT, CP Ajao Adewale, ya yaba da jajircewa da ƙwarewar jami’an wajen tabbatar da an samu adalci duk da tsawon lokacin. Ya gargaɗi masu aikata laifi da su daina ko su bar Abuja, yana mai cewa doka za ta kama su ko da yaushe. Rundunar ta kuma tabbatar wa mazauna FCT cewa tsaronsu na da muhimmanci tare da roƙon su riƙa bayar da bayanai kan duk wani abin da suke zargi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp