Jami’an rundunar Ƴansandan jihar Kwara sun kama Abdulrahman Bello, wanda ake zargi da kisan Hafsoh Lawal, dalibar da ke shirin kammala karatu a Kwara State College of Education, Ilorin.
A cewar rahoton jaridar LEADERSHIP, an gano gawar Hafsoh da aka sassara a wani gida da ke Ilorin bayan an nemeta ba a ganta ba tun ranar Talata.
Mai magana da yawun ‘yansanda, Toun Ejire-Adeyemi, ya tabbatar da kama Abdulrahman Bello mai shekaru 25 a wani bayani da ya fitar a ranar Lahadi.
Yadda Aka Kama Wanda Ake Zargi
‘Yansanda sun bayyana cewa an fara neman Hafsoh ne bayan mahaifinta Ibrahim A. Lawal ya kai rahoto cewa ta fita halartar bikin suna a ranar 10 ga Fabrairu, 2025, amma ba ta dawo gida ba. Duk ƙoƙarin kiran wayarta ya ci tura.
Bayan bincike ta hanyar fasaha, an gano inda wayarta take, wanda hakan ya kai ga kama Abdulrahman Bello. Lokacin da aka kama shi, ya amince da laifin kisan Hafsoh da nufin yin sihirin kudi (oshole/ajoo owo).
A binciken da aka yi a gidansa, an samu:
Wayoyi biyu da takalmin mamaciyar
Hannaye da aka sare daga jikin gawarta roba mai dauke da jininta
Adda, wuka, gatari, da akwatin sihiri
Buhun tsafi da tebur da aka yi amfani da shi wajen aikata kisan
An tura Abdulrahman zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) Ilorin, domin zurfafa bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.
Mai martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana takaici kan wannan ɗanyen aiki, yana mai cewa “abin baƙin ciki ne, kuma yana da ban tsoro”.
Ya buƙaci iyaye su ƙara sa ido kan ‘ya’yansu, tare da kula da irin mutanen da suke mu’amala da su.