Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, ya bar shalƙwatar Ƴansanda ta (IRT) da ke Abuja bayan ya amsa gayyatar da aka yi masa dangane da zargin ɗaukar nauyin ta’addanci, da laifukan yanar gizo, da cin amanar ƙasa, da haɗin baki wajen aikata laifi, da laifin cin amanar kasa.
Ajaero ya isa shalƙwatar ne IRT tare da shugabannin NLC kafin ƙarfe 10 na safiyar yau Alhamis kuma ya bar ofishin da misalin karfe 11:15 na safe bayan ya rubuta bayani. Ko da yake bai yi wa ‘yan jarida jawabi ba a shalƙwatar IRT, Ajaero ya nuna cewa zai yi magana daga baya a shalƙwatar NLC.
- Lallai A Hukunta Waɗanda Suka Kai Mamaya Ofishin NLC – TUC
- Kungiyar NLC Ta Nemi Rundunar ‘Yansanda Ta Nemi Afuwarta
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Ƴansanda sun gayyaci Ajaero zuwa shalƙwatar IRT a ranar 20 ga watan Agusta don amsa waɗannan zarge-zargen masu tsanani. Sai dai, saboda wasu dalilai, Ajaero bai samu damar halarta a ranar da aka tsara ba, amma ya yi alƙawarin amsa gayyatar a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta.
Kafin ya bar Ofishin ƙungiyar ƙwadago, an ga Ajaero tare da lauyoyin NLC da manyan shugabannin ƙungiyar, ciki har da Babban Lauya mai lambar (SAN) Femi Falana, da Marshal Abubakar, da Deji Adeyanju, da wasu manyan jami’an NLC. Sun nufi ofishin IRT da ke tsohuwar mayanka, kusa da mararrabar Guzape, Abuja.