Ɓarayin waya sun kashe wani ɗalibin koyon aikin jarida mai suna Samuel Mbami, wanda ke aji biyu (ND2) a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta ATAP, a Jihar Bauchi.
Lamarin ya faru ne cikin a daren ranar Juma’a lokacin da wasu da ake zargin masu ƙwacen waya ne suka kai hari gidajen haya guda biyu da ɗalibai ke kwana a unguwar Wuntin Dada.
- Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12
- Kamfanin Novo Nordisk Na Denmark Zai Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar Sin A Bana
Wani ya ce ɓarayin sun yi arangama da marigayin ne a lokacin da suka shiga gidan.
Wanda a nan ne suka kashe shi.
Shugaban ƙungiyar ɗalibai na kwalejin, Usman Aliyu, ya tabbatar da kisan tare da yin Allah-wadai da lamarin.
Ya ce suna roƙon gwamnati da hukumomin tsaro su gudanar da bincike don gano waɗanda suka aikata laifin da kuma ƙara tsaro a inda ɗalibai ke kwana.
Ya kuma yi kira ga ɗalibai da su kwantar da hankali, sannan suke ɗaukar matakan kare kansu.
Kakakin ’yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya bayyana cewa Kwamishinan ’yansandan jihar, Sani-Omolori Aliyu, ya ziyarci kwalejin domin jin ta bakin shugabancin makarantar da kuma duba hanyoyin magance irin wannan matsala.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp