ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar

by Abubakar Sulaiman
11 months ago
APC

Watanni uku bayan zaɓensa a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, har yanzu ana nuna Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin Ministan harkokin jin ƙai da rage talauci a shafin yanar gizon ma’aikatar.

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa muƙamin da Yilwatda ya riƙe kafin zama shugaban jam’iyyar shi ne Ministan harkokin jin ƙai da rage talauci. Sai dai binciken da aka gudanar a ranar Alhamis ya nuna cewa har yanzu bayanansa suna kan shafin ma’aikatar, inda ake kiran sa da “Hon. Minister, Prof. Nentawe G. Yilwatda.” Shafin har yanzu yana ɗauke da cikakkun bayanai kan aiyukansa a matsayin minista, duk da cewa ya hau kujerar shugabancin APC tun watan Yuli.

  • Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban APC Na Ƙasa, Farfesa Yilwatda
  • Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa

An zaɓi Yilwatda a matsayin shugaban jam’iyyar APC a ranar 24 ga Yuli, 2025, a taron majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) da aka gudanar a Abuja. An gabatar da sunansa daga Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, kuma kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya mara masa baya kafin a rantsar da shi nan take.

ADVERTISEMENT

Sai dai har yanzu Ma’aikatar harkokin jin ƙai da rage talauci ba ta sabunta shafinta don cire bayanan sa ba. Bugu da ƙari, har yanzu shafin Facebook na ma’aikatar yana amfani da tsohon sunansa — Federal Ministry of Humanitarian Affairs, Disaster Management, and Social Development — duk da sauyin suna da gwamnati ta yi a farkon shekarar.

A halin yanzu, kujerar minista da Yilwatda ya bari tana jiran sabon mai riƙe ta, kuma an ambaci Bernard Mohammed Doro daga Jihar Plateau a matsayin wanda ake ganin zai gaje shi. Duk da haka, babu wata sanarwa da ta fito daga ma’aikatar ko jam’iyyar APC kan wannan kuskuren bayanai a hukumance.

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

APC
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su
  • Abubakar Sulaiman
    Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya
  • Abubakar Sulaiman
    Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
APC
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
APC
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Next Post
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026
Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

September 11, 2026
Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.