An saki ɗan jarida, Ibrahim Ɗan’uwa Rano, bayan da ƴansanda suka tsare shi a shalƙwatar Rundunar Ƴansanda ta Zone 1 Kano bisa zargin batanci ga wani mutum.
Sakin nasa ya biyo bayan suka da matsin lamba daga ƙungiyoyin fararen hula irinsu Cibiyar Fasahar Bayanai da Ci Gaban Jama’a (CITAD), da Amnesty International, da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, waɗanda suka bayyana tsarewar tasa a matsayin mataki na keta haƙƙin ɗan Adam da kuma yunƙurin danne ƴancin ƴan jaridu.
- Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna
- Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya
Ƙungiyoyin sun buƙaci a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba, suna mai cewa tsarewar ta saɓawa dokar kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma ƙa’idojin kare ƴancin ƴan jarida na ƙasa da ƙasa.
Sun kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su daina amfani da ƙarfin gwamnati wajen tsoratarwa ko hana ƴan jarida yin aikinsu cikin gaskiya da riƙon amana.