Matatar man fetur ta Ɗangote ta rage naira 65 a farashin man da take siyarwa, inda yanzu man da kamfanin ya ke fitarwa ya koma naira dari takwas da ashirin da biyar (825) daga naira ɗari takwas da casa’in (890).
Sabon farashin zai fara ne daga ranar 27 ga watan Fabrairu na shekara ta 2025 kamar yadda sanarwar ta tabbatar.
- An Haramta Wa Tankokin Man fetur Da Ke Jigilar Lita 60,000 Zirga-zirga A Faɗin Titunan Nijeriya
- Matatar Man Ɗangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦890
A cewar kamfanin Ɗangote, ragin ya samo asali ne sakamakon azumin watan Ramadan da ya ke kusantowa da kuma taimakawa gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu wajen rage wahalhalun da al’umma suke sha.
Ko a farkon wannan watan sai da kamfanin ya rage farashin man da take fitarwa domin saukakawa al’umma.
A watan Disamban shekarar da ta gabata kamfanin ya rage naira 70 akan kowace lita daga naira 970 zuwa 899 don bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Sakamakon wannan ragin da aka samu, yanzu gidan mai na MRS zai sayar da man a jihar Legas a kan naira 860, sai mutanen da suke yankin kudu maso yamma kuma da za su saya a kan naira 870, sai kuma mutanen Arewa da za su saya a kan naira 880, sai mutanen kudu maso kudu da kudu maso gabas da za su saya akan naira 890.
Kamfanin ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su taimaka wajen ganin sauƙin ya je inda ake bukata, domin an yi ragin ne don sauƙaƙawa al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp