Majalisar Dattawan Nijeriya ta ɗage zaman jin ra’ayin jama’a da aka shirya a yankin Arewa maso Yamma domin gyaran kundin tsarin mulki, a matsayin girmamawa ga marigayin dattijo kuma mai bayar da taimako, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu a makon nan.
Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya bayyana hakan a zaman ranar Talata, inda ya ce matakin ya biyo bayan tuntuba da masu ruwa da tsaki a yankin.
- Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina
- Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Isa Saudiyya Don Halartar Jana’izar Ɗantata
Akpabio ya ce, “Saboda rasuwar mashahurin mai taimako kuma jigo, Alhaji Aminu Dantata, wanda aka binne shi yau a Saudiyya, mun yanke shawarar dakatar da zaman da nufin girmamawa gare shi.
”Ya bayyana cewa za a sanar da sabuwar ranar taron nan gaba bayan tattaunawa da shugabanni a yankin. Sanata Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar kuma shugaban kwamitin gyaran kundin tsarin mulki, yana Saudiyya a halin yanzu kuma ana sa ran dawowarsa kafin a sanar da sabon lokaci.
Duk da ɗagewar taron a Arewa maso Yamma, sauran yankuna za su ci gaba da gudanar da zaman jin ra’ayin jama’a kamar yadda aka tsara a ranar 4 da 5 ga Yuli. Yankunan da za a gudanar da taron sun haɗa da: Lagos (Kudu maso Yamma), Enugu (Kudu maso Gabas), Ikot Ekpene (Kudu maso Kudu), Jos (Arewa ta Tsakiya), da Maiduguri (Arewa maso Gabas).
A yayin zaman, ana sa ran tattauna batutuwa da dama da suka haɗa da ’yancin ƙananan hukumomi, ƙirƙiro hukumar zaɓe ta ƙasa don kula da zaɓen ƙananan hukumomi, kafa ƴansanda na jihohi, da ƙara yawan kujerun mata a majalisun dokoki domin samun wakiltar jinsin mata. Haka kuma, za a duba ƙuduri guda shida da suka shafi inganta gaskiya da rikon amana a harkokin kuɗi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp