Ɗaruruwan mambobin jam’iyyar APC mai mulki a ƙaramar hukumar Gada ta jihar Sokoto sun fice daga jam’iyyar, sun koma jam’iyyar ADC, suna danganta dalilinsu da tsananin rashin tsaro, talauci da kuma gazawar gwamnati.
A ranar Lahadi aka karɓe su a hukumance ta hannun Sanata Abubakar Gada, babban jigo a tafiyar haɗin gwiwar ADC, wanda ya bayyana wannan mataki a matsayin alamar ƙarin gajiya da fushin jama’a ga gwamnatin APC.
- Zaben Cike Gurbi: Tinubu Ya Lalata Tsarin Zaben Nijeriya — ADC
- Nasarar APC A Zaɓen Cike Gurbi Ta Tabbatar Da Sahihancin Mulkin Uba Sani – Mai Yaki
“Mutanenmu suna fuskantar matsanancin rashin tsaro wanda ya lalata harkar noma, wacce ita ce ginshiƙin tattalin arzikinmu. Wanda hakan ya janyo talauci, da rashin aikin yi, da yunwa a cikin al’umma,” in ji Gada yayin da yake jawabi ga sabbin mambobin.
Ya bayyana cewa yawan masu sauya sheka zuwa ADC ba kawai nuna rashin gamsuwa da aikin APC ba ne, har ila yau shaida ce ta shirye-shiryen jama’a na mara baya ga wata sabuwar hanya.
“Yanzu mutane da dama na shiga ADC saboda suna gasgata da tafiyar haɗin gwiwarmu na ceto ƙasa. Gazawar gwamnatin APC ta tilasta wa ƴan Nijeriya su nemi sauyi don samun adalci a wani wuri, kuma ADC ce zata bayar ke ba da adalci,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp