Ɗaruruwan mambobin jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Gada ta Jihar Sakkwato, sun fice daga jam’iyyar, tare da komawa jam’iyyar ADC.
Sun ce sun bar APC ne saboda matsalar tsaro, talauci, da kuma rashin kyakkyawan shugabanci.
- An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing
- Ƙungiyar KSCI Ta Nemi Sabon Tsari Don Magance Ƴan Bindiga A Katsina
An karɓe su a hukumance a ranar Lahadi ta hannun Sanata Abubakar Gada, ɗaya daga cikin manyan shugabannin haɗakar ADC.
Ya ce wannan lamari alama ce ta yadda mutane da dama ke gamsuwa da rashin nagartar gwamnatin APC.
“Mutanenmu na fama da matsanancin rashin tsaro wanda ya lalata noma, wanda shi ne ginshiƙin tattalin arziƙinmu. Wannan ya jawo talauci, rashin aikin yi da yunwa a cikin al’umma,” in ji Gada yayin taron.
Ya ƙara da cewa jama’a na shiga ADC saboda suna ganin ita ce mafita.
“Gazawar gwamnatin APC ta tilasta mutane su nemi mafita, kuma ADC za ta bayar da wannan damar,” in ji shi.