Ɗan wasa Mahamadou Diawara, ɗan ƙasar Faransa, ya fice daga sansanin ‘yan wasan ƙasar na ƙasa da shekara 19 bayan da hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar, ta saka wata dokar hana kowanne ɗan wasa yin azumi a cikin a lokacin ɗaukar horo da tawagar ‘yan wasan ƙasar.
Ƙasashe da dama dai suna bai wa ‘yan wasa Musulmi dama ta yin azumi yayin da wani lokacin ma a kan tsaya ana tsaka da wasa cikin watan Ramadan domin bai wa ‘yan wasa Musulmi damar yin buɗa baki.
- Tsaron Iyakoki: ACG James Sunday Ya Jagoranci Taron Samar Da Dabarun Aiki A Jos
- Zulum Ya Rabawa ‘Yan Sa Kai Da Mafarauta 5,523 Naira Miliyan 255 Da Buhunan Shinkafa 5,513
A farkon wannan watan ma ana tsaka da wasa a gasar Bundesliga ta ƙasar Jamus an tsaya ana tsaka da wasa domin bai wa Musulmi damar shan ruwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp