ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 22, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

by Sulaiman and Shehu Yahaya
12 seconds ago

Ba Mu Da Wata Yarjejeniya Da Wani Ɗan Takara – TIGMEIN

Kungiyar Wayar Da Kai Da Ci gaban Mabiya Darikar Tijjaniyyah ta kasa (TIGMEIN) ta bayyana cewa ba ta kulla wata yarjejeniya da wani dan takarar siyasa ko jam’iyyar siyasa ba a halin yanzu, dangane da babban zaben shekarar 2027.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar na jihar Kaduna, Malam Nasir Bello, yayin taron masu ruwa da tsaki na TIGMEIN wanda aka gudanar a Kaduna.

ADVERTISEMENT

Bello ya ce kungiyar tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, amma har yanzu ba ta yanke shawarar jam’iyyar ko dan takarar da za ta mara wa baya a zaben 2027 ba.

Yace an shirya taron ne domin yin nazari akan shugabanci da kuma makomar kungiyar a zaben shekarar 2027 inda yace kungiyarsu tana da gudummawar take bayarwa a zabukan Kasar Nan.

LABARAI MASU NASABA

Saudiyya Za Ta Fara Jigilar Fasinjoji Kai Tsaye Daga Abuja Zuwa Jeddah

Dalilin Da Ya Sa NPA Ta kirkiro Da Tsarin Ajiye Manyan Kaya A Tashohin Ƙasar

A cewarsa, TIGMEIN kungiya ce da ke da alaka da jam’iyyun siyasa daban-daban a fadin Nijeriya, ba tare da nuna wariya ga kowace jam’iyya ba.

Ya kara da cewa gayyatar wakilan jam’iyyun siyasa daban-daban, ciki har da jam’iyya mai mulki da jam’iyyun adawa, zuwa taron na daga cikin kokarin samar da fahimtar juna da tattauna hanyoyin hadin gwiwa.

Bello ya kuma bayyana cewa kungiyar ta tsara dabarun wayar da kan jama’a da suka hada da kananan hukumomi, mazabu, rumfunan zabe da al’ummomi, tare da gudanar da ziyara gida-gida domin tuntubar mambobi da magoya bayanta.

Ya jaddada cewa babu wata yarjejeniya da aka cimma da wani dan takara a yanzu, yana mai cewa shugabancin kungiyar ne zai sanar da matsayar karshe bayan kammala shawarwari da tantance dukkan batutuwan da suka dace.

Ya bukaci mambobi da magoya bayan kungiyar da su guji daukar matakin siyasa da kansu ko yada bayanan da ba su fito daga shugabancin kungiyar ba, tare da ci gaba da kasancewa cikin hadin kai da jiran sanarwar hukuma kan matsayarta a babban zaben 2027.

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    An Yi Taron Dandalin Tattaunawa Kan Nazarin Tunanin Tsarin Gurguzu A Kasar Sin
  • Sulaiman
    Saudiyya Za Ta Fara Jigilar Fasinjoji Kai Tsaye Daga Abuja Zuwa Jeddah
  • Sulaiman
    Dalilin Da Ya Sa NPA Ta kirkiro Da Tsarin Ajiye Manyan Kaya A Tashohin Ƙasar
  • Sulaiman
    ’Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Hana Gudanar da Zaɓen 2027 A Wasu Al’ummomin Zamfara
Shehu Yahaya
+ postsBio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Ayyukan Tinubu A Kaduna Sune Dalilanmu Na Sake Zaɓensa A 2027 – Maiyaki
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Ƙungiya Ta Fara Horas Da Mata Kan Yadda Ake Kaɗa Ingantacciyar Ƙuri’a Domin Kauce Wa Lalacewarta
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Shehu ABG Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gwamna A Kaduna
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Kotu Ta Ba Da Belin Ƴar Jarida Farida Isiak Bayan Tsare Ta A Kaduna
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Saudiyya Za Ta Fara Jigilar Fasinjoji Kai Tsaye Daga Abuja Zuwa Jeddah
Labarai

Saudiyya Za Ta Fara Jigilar Fasinjoji Kai Tsaye Daga Abuja Zuwa Jeddah

November 22, 2026
lekki
Labarai

Dalilin Da Ya Sa NPA Ta kirkiro Da Tsarin Ajiye Manyan Kaya A Tashohin Ƙasar

November 22, 2026
‘Yan Ta’adda Sun Yi Wa Tawagar ’Yansanda Kwanton Ɓauna A Hanyar Zamfara
Labarai

’Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Hana Gudanar da Zaɓen 2027 A Wasu Al’ummomin Zamfara

November 22, 2026

LABARAI MASU NASABA

November 22, 2026
An Yi Taron Dandalin Tattaunawa Kan Nazarin Tunanin Tsarin Gurguzu A Kasar Sin

An Yi Taron Dandalin Tattaunawa Kan Nazarin Tunanin Tsarin Gurguzu A Kasar Sin

November 22, 2026
Labour Party Ta Yi Alƙawarin Samar Da Shugabanci Nagari A Nasarawa

Labour Party Ta Yi Alƙawarin Samar Da Shugabanci Nagari A Nasarawa

November 22, 2026
Saudiyya Za Ta Fara Jigilar Fasinjoji Kai Tsaye Daga Abuja Zuwa Jeddah

Saudiyya Za Ta Fara Jigilar Fasinjoji Kai Tsaye Daga Abuja Zuwa Jeddah

November 22, 2026
lekki

Dalilin Da Ya Sa NPA Ta kirkiro Da Tsarin Ajiye Manyan Kaya A Tashohin Ƙasar

November 22, 2026
‘Yan Ta’adda Sun Yi Wa Tawagar ’Yansanda Kwanton Ɓauna A Hanyar Zamfara

’Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Hana Gudanar da Zaɓen 2027 A Wasu Al’ummomin Zamfara

November 22, 2026
Waɗanne Abubuwa Ne Suka Bambanta Tarbiyyar Wannan Zamani Da Ta Da?

Waɗanne Abubuwa Ne Suka Bambanta Tarbiyyar Wannan Zamani Da Ta Da?

November 22, 2026
Na Yi Sahu Jere Da Liman, Yaya Ingancin Sallata?

Na Yi Sahu Jere Da Liman, Yaya Ingancin Sallata?

November 22, 2026
Kamfanin Haƙar Ma’adinan Gawayi Na Dangote Ya Raba Tallafin Karatu Ga Dalibai A Jihar Kogi

Kamfanin Haƙar Ma’adinan Gawayi Na Dangote Ya Raba Tallafin Karatu Ga Dalibai A Jihar Kogi

November 22, 2026

Mijina Ba Ya Son Haihuwa, Ya Halatta Na Hana Shi Kaina?

November 22, 2026

© 2026 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2026 Leadership Media Group - All Right Reserved.