Wata Kungiya da ke goyon bayan shugaban kasa (PSC), Muhammadu Buhari, ta bukaci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya dora kan irin aiyukan Buhari a gadon mulki don samun nasara da zarar an zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.
Kungiyar ta bada wannan umarni ne a Abuja a wani taron manema labarai da shugabanta na kasa Hon. Gideon Sammani da Sakataren Yada Labarai na Kasa, Dr Muhammad Kailani, suka gudanar.
- Yanzu-yanzun: Tinubu Ya Kai Wa Buhari Ziyara A Fadarsa Abuja
- 2023: Ban Zabi Kowa Ba, Ban Kuma Yarda A Kakaba Dan Takara Ba —Buhari
Kailani ya ce ‘yan Nijeriya na fatan Tinubu zai hada kan ‘yan Nijeriya tare da tabbatar da cewa ya dauki dukkan ‘yan kasar domin samun nasara.
Ya taya Tinubu murnar fitowar sa a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Ya kuma yabawa tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio kan ya ajiye takararsa ga Tinubu, wanda ya ce hakan ya taimaka matuka wajen nasarar Tinubu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp