Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jamiyyar PDP, Alh. Atiku Abubakar, ya mayar da martani kan wani labari da yake yawo cewa ya dauki tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, a matsayin matainakinsa.
Labarin na nuni da cewa, bayan Atiku ya lashe zaben fidda gwani a PDP don yin takarar shugaban kasa, ya shirya tsaf don daukar Ihedioha a matsayin wanda zai wanda zai dafa masa a takararsa.
- Yayin Da Atiku Ya Zama Kwamandan PDP A 2023…Kallo Ya Koma APC
- 2023: Ni Kadai Ne Zan Iya Kawo Kuri’un Da Za Su Kayar Da Atiku —Rochas
Atiku ya mayar da martanin ne ta bakin kakakinsa, lPaul Ibe, inda ya ce ubangidan nasa, bai dauki Ihedioha a matsayin mataimakinsa ba.
A cewarsa, Atiku zai sanar da sunan mataimakinsa idan lokacin ya yi, inda ya sanar da cewa jama’a su daina yada labaran kanzon Kurege kan maganar Atiku ya dauki wanda zai masa mataimaki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp