Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku/Okowa ya baiwa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) tabbacin cewa ba sai ta damu da wani shirin zagaye na biyu na kada kuri’a ba, a zagayen farko dan takararta zai lashe zaben.
Kwamitin ya bukaci INEC da kada ta saurari bayanan karkatar da hankalin mutane da jam’iyyar APC ke yi, kawai suna neman hanyar da za su iya kawo cikas ne a zaben, bayan sun fahimci cewa jama’a sun yi watsi da jam’iyyar su.
Kwamitin yakin neman zaben na PDP ya ci gaba da cewa ya kamata INEC ta yi amfani da duk kayan aikinta da basirarta wajen gudanar da zabe mai inganci da gaskiya wanda galibin ‘yan Nijeriya za su aminta da shi.
Kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa, Kola Ologbondiyan, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce: “Kamfen dinmu na da yakinin cewa bisa dukkan alamu da bayanan da ake da su, dan takararmu, Atiku Abubakar, zai lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Fabrairu, 2023 a zagaye na farko.”