Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin da yamma, ya share duk wani shakku kan matsayarsa akan zaben dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, inda ya bayyana a gaban gwamnonin jam’iyyar 14 na jihohin Arewa cewa ba shi da dan takarar da ya fi so, kuma bai yarda a kakaba dan Takara ba.
A jawabin da ya yi da gwamnonin a fadar gwamnati da ke Abuja, Shugaba Buhari ya ce jam’iyyar na da muhimmanci kuma dole ne a mutunta mambobinta.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce ya na sane da duk abin da yake yi, ya kuma bukaci gwamnonin APC su fahimce shi da hakan.
“An zabe ku kamar yadda aka zabe ni. Allah ya bamu dama; ba mu da dalilin yin korafi. Dole ne mu kasance a shirye don daukar kaddara mai kyau da akasinta.
“Kuba wa wakilai dama su zabe wanda ya dace. Babu wanda zai nada kowa,” in ji shi.