Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Manjo-Janar Aminu Bande (mai ritaya), ya kaddamar da kwamitin kamfe dinsa a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.
Janar Aminu Bande a cikin jawabinsa ya yi alkawarin gudanar da dunkulalliyar gwamnati idan aka zabe shi a zaben 2023 mai zuwa a matsayin gwamnan Jihar kebbi.
- Ganduje Ya Kaddamar Da Manyan Motocin Sufuri 100 Da Kanana 50 A Kano
- Wani Harin Bam Ya Yi Sanadin Kashe Aƙalla Mutum 100 A Somaliya
Bande ya ce, “Takararta ba don son rai ba ce, a’a, don ci gaban jihar cikin gaggawa ne.”
Haka kuma ya yi alkawarin yin adalci ga kowace irin al’umma a fadin jihar ba tare da la’akari da addini, kabila da jam’iyya ba da nufin kai jihar ga wani babban mataki da kuma na ci gaba.
Dan takarar ya bukaci ’yan kwamiti yakin neman zaben da su dauki wani sabon salo na yakin neman zabe wanda kowane shugaba da kowane mamba zai kawo da rumfunansa ko rumfarsa na zabe a mazabar da ya ke jefa kuri’a, inda ya kara da cewa duk wanda bai iya kawo rumfar zabensa ba, to bai cancanci zama dan majalisar yakin neman zabensa ba ko yana da wani tasiri ga siyasa ba a yankinsu ko karamar hukumarsu.
Kazalika, ya shaida wa taron cewa, “Idan masu rike da madafun iko suka kawo musu kudi su karba, domin naku ne, amma ku tabbatar kun zabe Jam’iyyar PDP domin samun zaman lafiya, ci gaba da kawo canji a jihar Kebbi da Nijeriya baki daya.”
A nasa jawabin shugaban Majalisar yakin neman zaben Gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Shehu-Geda ya yi kira ga ’yan kwamiti da su jajirce da kuma nuna kwazo wajen ganin Jam’iyyar PDP ta lashe dukkan mukamai na zaben 2023 mai zuwa a Jihar kebbi da na shugaban kasa.
Ya bayyana jin dadin yadda dukkan jiga-jigan siyasa a jihar Kebbi sun hallara, don haka ya tabbatar da cewa PDP ta riga ta lashe zabe a Jihar ta Kebbi da yardar Allah.
Kazalika, Shehu-Geda ya nemi goyon baya da hadin kan kowa da kowa domin samun nasarar zabe a fadin jihar.
Alhaji Bala tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar ya ce: “Yanzu na gamsu cewa PDP ta riga ta lashe dukkan mukaman zabe duba da irin manyan da na gani a nan.
“Duk da haka, ina so in roki dukkan ku da ku koma gida ku shawo kan jama’ar ku don su zabi jam’iyyarmu ta PDP a dukkan mukamai na zaben 2023.”
A nasa bangaren kwamishinan hukumar kula da tasrin gurabun daukar aikin gwamnati na tarayya mai wakiltar jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Atiku-Bubu ya bukaci sauran jam’iyyun siyasa da su gudanar da yakin neman zabensu cikin tsafta da kuma limana da kwanciyar hankali batare da wata fitina ba.
Ya ce sun yanke shawarar kafa tanti da PDP ganin yadda tsohon Janar din ya kasance a jam’iyyar ne domin ya kawo hayyaci da kuma canjin da ake so a jihar Kebbi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp