Gwamnan jihar Adamawa, Ahmad Umar Fintiri, kuma dan takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar PDP a karo na biyu, zai dauki Madam Hannutu Kadala, a matsayar mataimakiyarsa a babban zaben 2023.
Majiyar LEADERSHIP HAUSA, ta tabbatar da cewa gwamna Ahmadu Fintiri, ya kai ga kammala tuntuba da shirye-shiryen daukar Misis Hannatu Kadala a mataimakiyar gwamna.
- ‘Yan Fashin Daji Sun Sace Shanu Sama Da 200 Da Raguna A Wata Gona A Jihar Sakkwato
- ‘Yan Bindiga Sun Tashi Garuruwa 30 A Zamfara Da Bayar Da Umarnin Tashin Wasu 5 A Jihar Filato
Bayanan da ke fitowa na bayyana cewa gwamnan ba zai tafi da mataimakinsa, Crowther Seth, a karo na biyu ba, saboda zargin da masa Crowther din na rashin iya mu’amala da jama’a.
“Hannutu Kadala, itace macen da jama’a suke so gwamna ya dauka a matsayin mataimakiyarsa a zaben 2023, idan gwamna ya dauke ta ya yi abinda jama’a suke so” inji majiyar.
Madam Hannutu Kadala, tsohowar malamar makaranta, ta taba zama kwamishiniyar ma’aikatar muhalli ta jihar, a lokacin tsohon gwamna Murtala H Nyako.
Akwai masu ganin daukan mace Hannatu Kadala, zai kawo sauyi a yanayin siyasar jihar, ganin yadda jam’iyyar APC ta tsayar da mace, kuma sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya Sanata Aishatu Dahiru Ahmad Binani takarar gwamna.
To sai dai kuma wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa biyo bayan matsin lamba da ake yi wa, Hajiya Aishatu Dahiru Binani, kan cewa ta dauki musulmi, Abdulrazak Namdas, a matsayin mataimaki, Binani tana son daukan Titsi Ganima, a matsayin mataimaki a yanzu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp