Kwanakin baya Shugaba Muhammadu Buhari, a wani taro da ya halarta a Owerri na Jihar Imo, ya nemi rundunar ‘yansandan Nijeriya su samar da cikakken tsarin da zai kai ga samar da sahihin sakamakon zabe a 2023, ya kuma nemi su nisanta kansu daga harkokin siyasa su kuma tabbatar da tsayuwa wajen kare tsarin dimokradiyya.
Shugaba Buhari ya bude taron kwanaki uku ne na horas da manyan hafsoshin jami’an ‘yansanda, inda ya bukaci a sake nazarin yadda suke gudanar da ayyukansu musamman ganin bazanar tsaron da ake fuskanta a halin yanzu don haka yakamata su jajirce wajen ganin an gudanar da sahihin zabe a shekasrar 2023.
- Ana Baje Kolin Shirye-Shiryen CMG A Taron Kafofin Watsa Labaran Kasa Da Kasa Karo Na Farko
- 2023: Wike Zai Goyi Bayan Peter Obi Ya Yi Watsi Da Takarar Atiku
Shugaba Buhari ya kuma lura da cewa, sai fa in kuri’un al’umma sun yi tasiri a zabe kafin al’umma su samu kwanciyar hankali tare da rungumar gwamnatin da ta samu nasara.
Ya kuma kara da cewa, za a iya tabbatar da hakan ne ta hanyar samar da cikakken kwarraru jami’an ‘yansanda da suka san ayyukansu suka kuma gudanar da aikin naka ba tare da nuna son rai ba.
‘A kan haka ne, nike umartar Babban Sufeton ‘yansanda da ya samar da shugabanci nagari tare da ba kowa hakkin gudanar da harkokinsa na siyasa, ta haka al’umma za su rungumi duk wanda ya samu nasara don yana nuna abin da al’umma suka zaba ke nan,” in ji shi.
Tabbas nasara ko rashin nasarar zaben 2023 ya danganta ne da yadda jami’an tsaronmu suka gudanar da ayyyukansu musamman ma ‘yansanda.
Haka kuma a bayyana yake cewa, Hukumar Zabe INEC tana kokarin samar da sabbin hanyoyi na zaman don gudanar da harkokin zabe.
Muna sane da yadda INEC ta samar da na’urar ‘Card Reader’, ‘BBAS’ da kuma hanyoyin aikawa da sakamakon zabe ta na’ura, mai kwakwalwa. Wadanda sun taimaka wajen dakile ayyyukan ‘yan banga, satar akwatin zabe, da yadda a wasu lokutta ake samun mutane na kada kuri’a fiye da sau daya, wanda hakan ya yi matukar taimakawa wajen kara wa sakamakon zabukka mutunci.
Duk da cewa, wadannan na’u’roriun ba bai ba za a iya karkatar da sub a ne anmma sun taimaka kwarai da gaske wajen tabbatar da wadanda al’umma suka zaba ne suka kai ga samu nasara a zabukkan da aka gudanar a ‘yan shekarun nan.
Abin taikaici a nan shi ne duk da irin kokarin da INEC ta ke yi, ‘yansiyasa na nan suna neman wasu hanyoyin gudanar da ayuukjansu na magudi a lokuttan zabe.
Cikin manyan matsalolin da harkokin zabe ke fuskanta a kasar nan shi ne yadda ba a bari al’umma su zabi wanda suke so ya mulke a dukkan matakai don kuwa masu kudi ke kwace harkar zabe inda suke dankarawa mutanen da suke so a kan al’umma don su biya musu bukata yayin da suka kai ga kujerar mulkin a dukkan matakai.
Wannan halayyar ta haifar da shugabanin da basu iya gudanar da mulki ba, basa kuma sa al’amarin al’umma a gaban su. Dole Nijeriya ta kauce ma wannan hanyar don babu wani cigaba da za a samu tare da bin wannan tsarin gaba daya.
Abin dadada rai anan shi ne yadda Shugaban Kasa Muhammdu Buhari ya yi alkawarin tabbatar da ya bar tarihin gudanar da sahihin zabe ba tare da cutar da wani bangare ba kamar yadda aka gudanar da zabukkan jihohin Ekiti, Osun, da Anambra, hakan kuma ya sanya wa ‘yan Nijeriya da dama sun fara gaskata Shugaba Buhari a kan wannan alkawari nasa.
Amma wani abin da aka lura da shi a zabukkan jihohin Ekiti da Osun shi ne batun nan na sayen kuri’a, wannan kuma yana neman ya karya daraja da mutuncin zabukkan da aka gudanar a ‘yan tsakanin nan.
Ra’ayin wannan jarifar shi ne, tabbas lamarin sayen kuri’a ya matukar karuwa hakan kuma na faruwa ne saboda yadda jami’an tsaro suka kasa kamawa tare da hukunta masu wannan mummunan sana’a, dole a kawo karshen wannan lamarin a nan take. Dole ne ‘yansnanda su yi aikinsu a kan masu saye da sayar da kuri’ar koda kuwa wane ne.
Tabbas, al’umma da dama kan yi tunanin cewa, ‘yansanda kan goyi bayan gwamnati a dukkan zabukkan da ake yi ne, wannan kuma yana faruwa ne saboda haka lamarin yake a zabukkan da aka gudanar a shekarun baya. Ba haka lamarin ya kamata ya kasance ba. Sukan kawar da fuskokinsu su yayin da jami’an gwamnati ke harkar sayen kuri’u a lokacin zabe. Cikin manyan dalilin haka shi ne don gwamantin tarayyar ke tanadar wa jami’an tsaron kudin gudanar da ayyuykansu.
Muna iyan tunawa da cewa, Babban Sufeton ‘Yansanda, Alkali Usman Baba, ya tabbatar wa da shugaban Nijeriya cewa, rundunar za ta yi amfani da sakamakon taron wajen samar da cikakken tsarin tsaron da jami’anta za su yi amfani da su don samar da sahihin zabe, ta haka za a tabbatar da tsarin mulkin dimokradiyya da kasar nan ta doru a kai.
Ya yi alkawarin cewa, tsarin da za su fito da shi zai karfafa tsarin zaben kasa ta yadda al’umma za su karbi sakamakoin zaben 2023 ba tare da wata matsala ba.
Ra’ayin wannan jaridar na tare da shugaban kasa inda ya nemi cewa, ya kamata sakamakon zabukkan 2023 ya zama abin da al’umma suka zaba ne, dole a gudanar da sahihin zabe da zai samu karbuwa ga dukkan al’umma. Wannan shi ne sirrin dimokradiyya.