Kwanan nan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fara horas da ma’aikatan wucin-gadi fiye da miliyan 1.2, domin su san makamar aikin gudanar da zaɓen 2023 da ke gaban su. Waɗannan ma’aikatan wucin-gadi ne tare da sauran ma’aikatan dindindin na INEC nauyin gudanar da sahihi kuma karɓaɓben zaɓe ke hannun su.
Kafin zuwan ranar zaɓe, ya kamata mai karatu ya san matsayi da ayyukan waɗannan ma’aikata a ranakun zaɓe.
Yayin da saura makonni biyu a jefa ƙuri’ar zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya, a ranakun 25 ga Fabrairu da 11 ga Maris, masu karatu za su so jin ayyuka, matsayi da muhimmancin wasu manyan jami’an Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a lokacin zaɓe.
Kwamishinonin Zaɓe Na Jihohi (RECs), waɗanda a Turance ake kira ‘Resident Electoral Commissioners’: Su ne INEC ta ɗora wa nauyin kula da kuma sa-ido wajen gudanar da zaɓuka a jihohi da FCT, Abuja.
Su ne kuma INEC ke damƙa wa kayan zaɓe na sirri da su ka haɗa da takardun sirri irin su ƙuri’u da sauran kayan aikin zaɓe. Su ne kuma ke rarraba su ga dukkanin jami’an gudanar da zaɓe. Kuma su ne ke da alhakin ɗaukar ma’aitakan zaɓe na wucin-gadi da kuma horas da su ƙa’idojin da su ka shafi aikin zaɓe.
Baturen Zaɓe: Shi Baturen Zaɓe, wato ‘Electoral Officer’ aikin shi gudanar da zaɓe da sa-ido kan zaɓen a ƙaramar hukuma ko gundumomi idan a FCT Abuja ne.
Kuma su na karɓar kayan aikin zaɓe daga hannun Kwamishinan Zaɓe na Tarayya a Jiha (REC). Su kuma za su raba wa Dubagarin Baturen Zaɓe (Supervisory Presiding Officers) su rarraba wa Jami’an Zaɓe (Presiding Officers)
Dubagarin Jami’an Zaɓe (Supervisory Presiding Officers): Aikin su shi ne sa-ido wajen kula da yadda ake gudanar da zaɓuɓɓuka a rumfunan zaɓe. Kuma su na taimakawa wajen horas da Jami’an Zaɓe da sauran su. Kuma aikin su ya haɗa da tabbatarwa dukkan kayan zaɓe sun isa rumfunan zaɓe a wadace kuma a kan lokaci.
Kuma aikin su ne su riƙa zagayawa rumfunan zaɓe daban-daban su na jin ko akwai ƙorafe-ƙorafen da wata rumfar zaɓe ke son a magance mata cikin gaggawa.
Haka nan kuma aikin waɗannan jami’ai ne su ga cewa lallai sakamakon zaɓen rumfunan zaɓen da ke ƙarƙashin su ya isa a cibiyar tattara sakamakon zaɓe daga hannun jami’in zaɓe zuwa hannun jami’in tattara sakamakon zaɓe (collation officer).
Sannan kuma aikin sa ne ya tabbatar an mayar da dukkan kayan zaɓe a hannun Baturen Zaɓe da zarar an kammala gudanar da zaɓe.
Jami’an Tattara Sakamakon Zaɓe: Su ne a Turance ake kira ‘Collation Officers’, kuma aikin su ya haɗa tattara sakamakon zaɓe tsakanin rumfunan zaɓe a cikin yankunan karkara da kuma mazaɓa sukutum.
Jami’an Zaɓe Masu Kula Da Rumfunan Zaɓe: Wato su ne ‘Presiding Officers’, waɗanda aikin su shi ne kula da yadda ake gudanar da zaɓe a rumfunan zaɓe.
Kuma dai ne masu tantancewa, ƙirgawa da bayyana sakamakon zaɓe a rumfunan zaɓe, bayan sun yi jadawalin sakamakon yawan ƙuri’un da kowace jam’iyya ta samu, tare da ƙididdige yawan adadin ƙuri’un a aka jefa.
Waɗannan jami’ai tilas su riga kowa zuwa rumfar zaɓe a ranar zaɓe, domin su tsara yadda komai zai tafi daidai, ciki har da wayar wa masu zaɓe kai dangane da yadda za su kaɗa ƙuri’a.
Sannan kuma aikin su ne damƙa wa mai jefa ƙuri’a takardar ƙuri’ar da zai dangwala yatsa a kan ta.
Daga nan zai tabbatar cewa wanda ya zai jefa ƙuri’a ya dangwala mata yatsa kafin ya jefa cikin akwatin tattara ƙuri’u.
Jami’an Taimaka Wa Masu Aiki Da Na’urori: Za su riƙa bayar da taimakon gaggawa a wurare daban daban-daban.
Su ne za su riƙa yin gaggawar kai ɗauki wurin da duk aka samu matsala da na’urar BVAS. Za su yi gaggawar gyarawa ko canja wadda ta wajaba a canja nan da nan.
Sannan aikin su tabbatar da sakamakon zaɓen da rumfar zaɓe ta fitar aka loda a shafin manhajar tattara sakamakon zaɓe.
Jami’an Daidaita Gungun Masu Jefa Ƙuri’a (Polling Team): Wannan tawaga ba ta rasa kaiwa mutum huɗu a kowace rumfar zaɓe. Za su binciki rajistar sunayen masu jefa ƙuri’a, miƙa ƙuri’a ga wanda zai dangwala mata yatsa da kuma tabbatar da cewa masu jefa ƙuria sun shiga layi.
Jami’an Kula Da Zaɓe: Waɗannan ma’aikatan INEC ne na dindindin. Aikin su shi ne duba yadda zaɓe ke gudana a shiyyoyi, Ƙananan Hukumomi da Mazaɓu.
Baturen Bayyana Sakamakon Zaɓe: Shi ne ‘Returning Officer’, wanda aka ɗora wa aikin bayyana sakamakon zaɓen Sanata, Majalisar Dokoki ta Tarayya da ta Jihohi, sai kuma bayyana sakamakon zaɓen gwamnoni.
Babban Baturen Bayyana Sakamakon Zaɓe: Wannan kuma shi ne Shugaban INEC na ƙasa. Shi ke tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa daga kowace jiha. Idan ya kammala tattarawar shi ne daga nan sai ya bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.