Wata kotun majistire mai lamba 3 a jihar Bauchi ta tura mawallafin jaridar yanar gizo ta WikkiTimes, Malam Haruna Muhammad Salisu zuwa gidan gyara hali kan zargin tayar da zaune-tsaye da munana wa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad.
Alkalin Kotun, Ahmed Musa shi ne ya aike da dan jaridan gidan yari har zuwa ranar Laraba domin yanke hukunci kan bukatar bayar da beli kan kes din da kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Aminu Alhassan ya shigar a kan dan jaridan.
‘Yansandan dai sun zargi dan jaridan da yin hayar wasu mata domin ganin an kawo tsaiko ga zaman lafiya da kuma tayar da zaune tsaye a kusa da rumfar zabe a kauyen Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri gami da zargin munana wa gwamna Bala a mazabarsa lamarin da ya saba wa sashi 114 na Final Kod.
Da aka gabatar da karar a ranar Talata, dan jaridan ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa tare da cewa ‘bai aikata laifi ba’.
Lauyan kariya, Idris Gambo (SG Idrees) ya gabatar da bukatar bada belin wanda ake zargi. Idris Gambo dai ya ce, bisa la’akari da zargin da ake yi wa Haruna, za a biya bada belinsa, don haka ne ya nemi kotun ta amince da bayar da belin nasa.
Amma lauyan masu kara ya yi suka bisa kan bukatar belin. Lauyan ya ce, abun da ya sanya suka ki amincewa da belin shi ne rayuwar Harunan na cikin hatsari domin wasu da suke waje suna zaman jiran su far masa ta hanyar daukan doka a hannu.
Sai dai Lauyan Haruna, Barista Gambo ya shure dukkanin batutuwan lauyan masu karan.
Yana mai cewa, kamatuwa ya yi gwamnati da ‘yansanda da su tashi tsaye su fuskanci wadanda ake ce su na shirin farmakar wanda yake karewa.
Sai dai kuma wani lauya daga ofishin Antoni-janar na jihar Bauchi, Haruna Ibrahim ya bayyana a gaban kotun inda ya sanar da cewa, Antoni-janar na shigar na son zai karbi ragamar cigaba da kes din daga hannun ‘yansanda domin cigaba bisa amfani da kundin tsarin mulkin kasa na 1999.
Daga bisani ne dai kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Maris domin cigaba da sauraron bukatar bayar da beli.
Rahotonni na nuni da cewa, an cafke Haruna ne a yayin da ake zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya a ranar Asabar inda ke daukan bidiyon wasu mata da ke zanga-zangar bayyana abun da ke damunsu a lokacin da ake gudanar da zaben a kusa da mahaiyar gwamna Bala a kauyen Duguri.
Sai dai, editan jaridar WikkiTimes, Yakubu Mohammed ya bayyana ta cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, gwamnan Bauchi, Bala Muhammad na da hannu a shari’ar, ya zargi gwamnan da kokarin tauye wa dan jaridan ‘yancinsa.