Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Hon Abdulaziz Yari Abubakar kuma dan takarar Sanata a shiyyar Zamfara ta Yamma, ya karyata zargin da wasu ke masa na yin Angulo da kan Zabo a zabe mai zuwa.
Inda ya tabbatar da cewa, duk mutanensa da magoya bayansa na cikin kananan hukumomin goma sha hudu da ke Jihar, sun aminta da zaben Jam’iyyar APC tun daga sama har kasa.
Yari ya bayyana hakan a jiya Lahadi a lokacin da dubban magoya bayan jam’iyyar APC suka tarbe shi a Talatan Mafara don fara tattaunawa da dukkan magoya bayan sa da fadin jihar ta Zamfara kan yadda za su tunkari yakin neman zabensa na 2023.
Abdulaziz Yari, ya shawarci dukkan magoya bayan jam’iyyar APC a fadin jihar da su tabbatar da goyon bayansu ga dukkan ‘yan takarar da za su fafata a zaben 2023 tun daga shugaban kasa har zuwa kansiloli domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a yayin zaben da ke tafe.
“Mun samu labarin cewa wasu ‘yan siyasa marasa kishin jam’iyyar sun amshi kwangilar domin yi wa Jam’iyyar APC zagon kasa a zabe mai zuwa da yarda Allah ba za su kai ga ci ba”, in ji Yari.
Tsohon Gwamnan ya ce ya shirya tsaf domin kaddamar da yakin neman zabensa na Sanata a shiyyar Zamfara ta Yamma da ta kunshi kananan hukumomin Gummi, Bukkuyum, Anka, Maradun, Bakura da Talata Mafara domin ganawa da masu rusa da tsaki dan ganin sun samu nasara a zabe mai.