Wasu rahotanni sun bayyana mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi watsi da takarar Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a matsayin ‘yan takarar APC a zaben 2023.
Wata majiya da ke kusa da mataimakin shugaban kasan, ta ce ya kafe kan kudurinsa na kin jinin takarar Musulmi biyu a zaben 2023.
- Haramtattun Kudaden Da Ke Yawo A Afirka Sun Karu Zuwa Dala Biliyan 80– CDD
- Daura Zan Koma Da Zama Idan Wa’adin Mulkina Ya Kare – Buhari
Majiyar ta ce Osinbajo tun a 2014 yake yaki da kin jinin tafiyar Musulmi biyu a matsayin ‘yan takarar jam’iyyar APC kafin daga bisani ya zama dan takarar mataimakin jam’iyyar.
An ruwaito ya ce “Duk tafiyar da za a yi hadakar da babu adalci a ciki, bana goyon bayanta.”
Tuni aka fara yada rade-radin cewar mataimakin shugaban kasar, ya fara tunanin hada tafiyar siyasa da dan shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
An ce dukka bangarorin biyu sun fara tattaunawa kan yadda za su yi tafiya tare don ciyar Nijeriya gaba.
Wata majiyar ta bayyana cewar tuni bangarorin biyu suka fara shirin ganawa don cimma matsaya.