Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP na Najeriya ta soke duka zabukan fitar da gwani da aka yi a jihar Ebonyi dake kudu maso gabshin kasar tana cewa za ta sake sanar da ranar da za a yi zabukan a nan gaba.
BBC Hausa ta rawaito cewa, cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar Hon Debo Ologunagba ya fitar ta ce, an dauki matakin ne bayan tuntubar da aka yi tsakanin kwamitin shirya zaben na jam’iyyar.
“Bayan sauraren juna da aka yi aka yi wa lamarin kallon tsakani, kwamitin shirya zaben ya amince da a soke duka zabukan fitar da gwani da aka yi a jihar Ebonyi.
“Da wannan muke sanar da cewa, duka wadanda aka zaba a matakin majalisar wakilai da zartarwa da gwamna a jihar Ebonyi duka an soke zaben.
Kwamitin shirya zabukan na PDP zai sanar da sabuwar rana da za a gudanar da zabukan shikin lumana,” in ji sanarwar.