Rashin halartar jiga-jigan ‘yan takarar shugaban kasa na jamiyyar APC mai mulki a taron zaman sulhu da uwar Jam’iyya ta kasa ta shirya, ya janyo tsaiko ga zaman sulhunta ‘ya’yan Jam’iyyar da suka yi takarar zaben fidda gwani.
Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da Shugaban Jam’iyyar APC dai a jiya Laraba ne suka shirya yin zaman sulhun a babban birnin tarayyar Abuja.
Tinubu ya sami nasarar lashe tikitin Shugabancin kasa a Jam’iyyar APC mai mulki ne, bayan karawarsa da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; da Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osibanjo da sauran ‘yan takara 12, wanda matashi daga cikin su, Dakta Nicolas Felix ya Nemi ayi zama na sulhun, domin a dinke barakar da takarar fidda gwanin ta haifar, acewarsa APC ta tunkari zaben 2023 gadan-gadan.
‘Yan takarar da aka gayyata zuwa zaman na sulhun sun hada da,Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi, Ogbonnaya Onu, Chukwuemeka Nwajiuba, Godswill Akpabio, Yahaya Bello, Dave Umah, Abubakar Badaru, Kayode Fayemi da Ben Ayade.
Sauran su ne, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan; tsohon Gwamnan jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amosun; Sanata Ajayi Boroffice; Sanata Ahmad Sani Yerima; tsohon Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha; tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Ken Nnamani, tsohon shugaban Majalisar Wakilai, Dimeji Bankole; Fasto Tunde Bakare; Dan kasuwa Dakta Nicolas Felix; tsohon Ministan Yada Labarai, Ikeobasi Mokelu; Dan kasuwa, Tein Jack-Rich sai kuma mace daya Uju Ken-Ohanenye.
Sai dai, a cikin sanarwar wacceya Dakta Nicolas Felix ya bukaci a zauna zaman sulhun, ya sanar da dage zaman sulhun, inda ya ce, za a sake sanar da wata sabuwar rana, gaba kadan.