Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya bayyana Sanata Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno, a matsayin abokin takararsa a zaben 2023.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a ziyarar da ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a garin Daura na jihar Katsina a ranar Lahadi.
A baya majiyar NAN ta Kawo rade-raden cewa Tinubu ya zabi Shettima kuma zai bayyana shi a matsayin sabon zababben mataimakinsa a takararsa ta neman shugaban cin kasa a cikin wannan mako. Inji Daily trust.
“Mai yiwuwa ne wanda Tinubu ya zaba a mataimakinsa a takarar shugaban kasa ya zama tsohon gwamna ne kuma Sanata daga yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya kuma musulmi ne, ya bayyana hakan ne yana mai tabbatar da abin da gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya fada a ranar Asabar din da ta gabata cewa, Tinubu ya amince ya zabi musulmi mataimakinsa a zaben 2023,’’ inji majiyar.
jim kadan kafin sanarwar da Tinubu ya yi a Daura, Alhaji Ibrahim Masari, wanda tun da farko aka tsayar da shi a matsayin abokin takararsa, ya bayyana ajiye mukaminsa a matsayin mataimakina dan takarar shugaban kasa a 2023.
Kafin janyewar tasa, an zabi Masari a matsayin abokin takarar Tinubu na dan wani lokaci domin ba wa dan takarar isasshen lokaci don tsayar da wanda yafi dace wa a zaben shugaban kasa a 2023.
Masari ya bayyana ajiye makamin ne a wata takarda da yasa wa hannu wacce ta fito daga Kasar Saudiyya.