Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya da cewa a zaɓen 2023 ta yi shirin yin fito-na-fito da masu sayen ƙuri’u, musamman a ranakun zaɓe.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke bayani a wani taro da hukumomin da ke ruwa da tsaki kan harkokin zaɓe, tsaro, rashawa da cin hanci a ranar Litinin, a Abuja.
Yakubu ya ce, “Mun san abu ne mai wahala sosai, ba mai sauƙi ba, to amma INEC za ta yi bakin ƙoƙarin ganin ta daƙile masu bayar da kuɗi su na sayen ƙuri’u.
“Wasu ba za su ji daɗin wannan kyakkyawan aikin da za mu yi na ƙara tsaftace zaɓe ba. Don haka su ma za su bijiro da na su dabarun. Sai dai kuma INEC za ta haɗa kai da ‘yan sanda, EFCC da sauran hukumomin tsaro domin su taimaka wajen kashe kaifin masu sayen ƙuri’u a wurin zaɓe ko kafin ranar zaɓen.”
Yakubu ya yi kira ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya masu jefa ƙuri’a cewa su tuna ƙuri’ar su fa ‘yancin su ce. Don haka ya ce su yi amfani da hankali da hangen nesa,su daina sayar da ‘yancin su a kan wasu ‘yan kuɗi ƙalilan waɗanda za su kashe a rana ɗaya.
Ya kuma hore su da su kai wa INEC da jami’an tsaro rahoton masu sayen ƙuri’u. Kuma ya yi kira ga ƙungiyoyin rajin kare haƙƙi su saka batun fallasa masu sayen ƙuri’u a jerin ayyukan sa-idon da za su yi kafin da kuma ranar zaɓen 2023.
Hukumomin da su ka shirya taron tare da haɗin gwiwar INEC, sun haɗa da ICPC, EFCC, BBC, Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya da Hukumar Ƙayyade Tsare-tsaren Tallace-tallace ta Nijeriya (APCON).