ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Zan Inganta Rayuwar Talakawan Gombe- Mailantarki Na NNPP

by Sulaiman
4 years ago
NNPP

A kwanakin baya ne ɗan takarar Gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, Khamisu Mailantarki ya bayar da gudummawar naira milyan 2.2 ga iyalan waɗanda ‘yan bindiga su ka kai wa farmaki a garuruwan Amtawalan da Paboure da ke ƙarƙashin gundumar masarautar Ƙaramar Hukumar Ɓilliri a jihar Gombe.

 

Ya bayar da tallafin ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje da ta’aziyya ga iyalan ƙauyukan guda biyu, a ranar Asabar, inda ya bayyana cewa wajibin duk wani mai tausayi ne ya tallafa wa waɗanda ke fama da bala’i.

ADVERTISEMENT
  • Da Dumi-Dumi: ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Gombe 2 Sun Fice Daga APC Sun Koma NNPP

Dangane da masu tururuwa zuwa cikin NNPP kuma, idan ba a manta ba cikin makon jiya ne Mailantarki ya kwashe baraden yaƙin Isyaku Gwamna, daga PDP su ka koma cikin rundunar NNPP.

 

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

A cikin wancan labarin, ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe a jam’iyyar NNPP, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya na ci gaba da karɓar dandazon manya da ƙananan magoya bayan APC mai mulkin jihar da kuma PDP.

 

A ƙarshen makon nan ne Mailantarki ya haska wa wasu manyan mambobin PDP hanya, su ka bi ta gwadaben da su ka koma NNPP.

 

Mambobin dai zaratan magoya bayan fitaccen ɗan siyasar nan ne Jamil Isyaku Gwamna, waɗanda ake kiran ƙungiyar su da suna Sardauna Dawo-Dawo.

 

A ranar Juma’a ce Mailantarki ya karɓi dandazon ‘yan PDP ɗin a bisa tarbar su da Shugaban NNPP na Jihar Gombe ya yi, wato Alhaji Abdulahi Maikano.

 

Wannan dandazon magoya baya dai sun canja sunan su daga Sardauna Dawo-Dawo zuwa Mailantarki Movement, bayan sauya sheƙar su daga PDP zuwa NNPP.

 

Sun bayyana cewa sun yanke shawarar goyon bayan ɗan takarar da “matashi ne mai jini a jika, wanda ke da jama’a a kowane ɓangaren al’umma, nagari na kowa, ƙwararre, kuma mai zuciyar tausayin al’umma.”

 

Shugaban tawagar mai suna Muhammad Makson ya bayyana cewa Gombawa ba su da wata matsala da Mailantarki, domin an jaraba shi a baya, kuma ya ci jarabawar riƙon amanar da aka damƙa masa.

 

“A kan haka, Mailantarki na da gogewar da zai iya magancewa da shawo kan matsalolin da su ka dabaibaye jihar Gombe.

 

“Gaba ɗayan mu ne mu ka yi shawarar ficewa daga PDP mu ka yanke shawarar dawowa cikin NNPP, saboda buƙatar ganin mun samu nagartaccen shugabancin da ya fi dacewa da Jihar Gombe.

 

“Mun yi amanna cewa Mailantarki ne zai iya tsamo Jihar Gombe daga kwazazzabon ramin da APC ta jefa jihar, sakamakon tuƙin gangancin da ake yi da motar da APC ta cika da lodin al’ummar Gombe.”

 

Makson ya ce waɗanda su ka fice daga PDP ɗin zuwa NNPP akwai shugabanni 2000, mambobi sama da 20,000 a faɗin mazaɓu 114 na Jihar Gombe.

 

Mailantarki ya tabbatar masu da cewa shi da NNPP za su tafi tare da su domin a gudu tare, a yi nasarar kafa gwamnati tare.

 

Daga nan ya roƙesu cewa sai sun ƙara tashi tsaye sosai wajen yaɗa manufofin NNPP da tallata ‘yan takarar jam’iyyar a cikin yankunan karkara, ta yadda za a kawar da gwamnatin APC a ranar zaɓen 2023.

NNPP
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post
Babu Matakin Da Muka Dauka Kan Murabus Din Okupe – Kwamitin Yakin Zaben Peter Obi

Babu Matakin Da Muka Dauka Kan Murabus Din Okupe - Kwamitin Yakin Zaben Peter Obi

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
NNPP

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
NNPP

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.