• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Za Mu Yi Amfani Da Na’urar BVAS Wajen Dakile Magudin Zabe – Farfesa Mahmood

by Sulaiman
3 years ago
BVAS

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta sha alwashin cewa yanzu haka ta na aiki tare da Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), domin magance duk wani cikas ɗin da za a iya fuskanta yayin aikawa da sakamakon zaɓen 2023 ta tsarin yaɗa sakamakon ƙuri’u ta BVAS.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya bayyana haka, ya na mai cewa an fara shiri tun a yanzu domin magance ko da wata matsala za ta bijiro saboda matsalar wuraren da saƙonni ta fasahar zamani ke wahalar isa, wato matsalar ‘network’.

  • Jerin Kayayyakin Da INEC Ta Yi Asara Bayan Kai Mata Hare-hare A Ofisoshinta

Yakubu ya bayyana haka a Legas, lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, a ranar Juma’a.

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

Wannan ƙarin haske da shugaban na INEC ya yi, ya biyo bayan damuwar da wasu ‘yan Nijeriya su ka fara nunawa cewa, za a iya samun matsala da tsarin BVAS a yankunan da ke fama da cikas ɗin samun saƙo ko yaɗa saƙon ta fasahar zamani.

BVAS
Taron INEC da manema labarai a Legas

Yakubu ya ce a ranar Talata INEC za ta gana da jami’an hukumar sadarwa (NCC), dangane da yadda za a magance matsalar da ka iya tasowa wajen aika sakamakon zaɓe ta hanyar amfani da BVAS.

Daga nan sai ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa kada su yi fargabar komai dangane da nagartar da zaɓen 2023 zai yi, ta hanyar amfani da BVAS.

“INEC ta gano waɗansu wuraren da ke da matsalar ingancin ‘network’ da kuma wuraren da babu ‘network’ ɗin kwata-kwata. Kuma mu na nan mu na aikin tabbatar da cewa ba a samu wata matsala wajen aika sakamakon zaɓen yankunan ba.

“Mu na ta aiki da jajircewar ganin tabbas mun aika dukkan saƙonnin sakamakon zaɓe ko ina a faɗin ƙasar nan,” inji shi.

Tun da farko sai da Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ya roƙi kakafen yaɗa labarai su taimaka wa hukumar zaɓen ta hanyar daƙile bayanan ƙarya da labaran shaci-faɗin da ake dangantawa da INEC.

Ya ce ga shi dai bai fi sauran kwanaki 85 a yi zaɓe ba, amma labaran bogin da ake yaɗawa kan INEC abin damuwa ne sosai.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

October 9, 2025
TCN
Labarai

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

October 9, 2025
Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI
Labarai

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Next Post
2023: Tinubu Na Gabatatar Da Jawabi Kan Zabe A Fadar Chatham Da Ke Ingila

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 9, 2025
TCN

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

October 9, 2025
An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

October 9, 2025
Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

October 9, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.