Farfesa Pat Utomi, Farfesa a fannin siyasa da tattalin arziki, ya ce an tattauna da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi; da na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar don shirin kafa wata babbar jam’iyyar adawa gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Ya ce manufar hakan ita ce, ceto talakawan Nijeriya daga kangin mulkin kama karya na jam’iyyar APC, wanda ya bayyana a matsayin wata kasuwa da tsirarun mutane ke zuba jari da gudanar da ita.
- Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar NNPP Na Kara Rincabewa A Kano
- Abin Da Ya Sa Muka Sa Takin Zamani Cikin Tallafin Jama’a – Gwamnan Filato
Utomi ya kara da cewa, siyasar Nijeriya na tabarbarewa ne saboda babu wata jam’iyyar siyasa da ke shirin baiwa kasar kyakkyawar alkibla.
“Mun tattauna da Peter Obi, Atiku Abubakar da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da sauran su kan yiwuwar dunkulewa a samar da babbar jam’iyyar adawa daya.
“Na gaya musu cewa, wannan tsarin ba don son kansu ba ne, sai don ceto ‘yan Nijeriya. Musamman talakawa da ke sintiri a kan titi.” Inji Utomi