A yayin da ya rage ‘yan kwanaki kotun koli ta yanke hukunci kan daukaka karar da Gwamnan Kano tare da Jam’iyyarsa NNPP suka yi, wanda suke kalubalantar hukuncin kotun sararon korafe-korafen zabe da kuma hukuncin da kotun daukaka kara suka zartar. Duka kotunan guda biyu sun bayyana Dakta Nasiru Yusuf Gawuna a matsyain halastaccen zababben Gwamnan Kano.
Yanzu haka dai lamarin na sake daukar sabon salo bayan yadda jam’iyyar NNPP da magoya bayanta suka rungumi tsarin addu’o’in samun nasara a kotun koli, bayan wani lokoci kuma suka shagala da batun zanga-zangar da suke toshe hanyoyin shigowa Kano da kuma yin sallar alkunuti.
- Kwace Wa NNPP Zaben Kano Na Iya Haddasa Tashin Hankali A Afrika – NNPP
- Zaben 2023: NNPP Ta Ci Zabe Ta Hanyar Magudi A Kano – Doguwa
Cikin makon da ya gabata, an wayi gari da kiraye-kiranyen zanga-zangar mata wadda hakan ya sa malamai suka fara tofa albarkacin bakinsu kan illar da ke tattare da umarnin fitowar mata zanga-zanga.
Babban limamin Masallachin Juma’a Na Triump wanda ya bayyana rashin da cewa fitowar matan musulmi zanga-zangar siyasa. Ya tambayi masu shirya zanga-zangar matan da cewa mai ya sa ba a ga matar gwamna da sauran matan mahukuntan gwamnatin ba.
A cikin abubuwan da ake kallo a matsayin sabon rikicin cikin gidan jam’iyyar ta NNPP, wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida cewa, gwamnatin Kano ta kori ma’aikata sama da dubu goma sha biyu wadanda gwamnatin baya ta dauka aiki.
Majiyar ta ce sakamakon rushe-rushe da gwamnati ta aiwatar ya haifar da mummunan bakin jini ga gwamnatin.
Ba a jima da fitar da wannan sanarwa ba sai gwamnatin ta sauya shawara, inda aka yi wa ma’aikatan fuskar shanu tare da kin dawo da su tsarin biyan albashin, abin da ya sa wani jami’in gwmanatin ya matsa lamba wajen shawartar gwamna domin cika wancan alkawari, wanda majiyar ta shaida cewa wannan kokarin tuna wa gwamna wancan alkawari ne ya haifar da wata gagarumar matsalar da a halin yanzu wasu hotuna ke ta yawo a kafafen sada zumunta, inda ake nuna wasu manyan jami’an gwamnati na musayar yawu tare da alkawarin za a saki cikakken faifan bidoiyon.