Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya yi watsi da ikirarin cewa, yana shirin komawa jam’iyyar adawa ta PDP.
Ganduje ya bayyana cewa, PDP ta mutu yayin da APC ke shirin samun gagarumar nasara a zaben 2027.
- Zamfara Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Kula Da Aikin 2025 Domin Kyautata Jin Dadin Alhazan Jihar
- Uwargidan Jonathan Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Remi Tinubu
Hakan dai ya biyo bayan ikirarin da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi na cewa, jam’iyyar APC za ta ruguje, kuma tsoffin ‘yan PDP da suka fice daga jam’iyyar, irinsa za su dawo.
Lamido a ranar Lahadi ya ce, “Ina da yakinin cewa duk wadanda suka bar PDP za su dawo ciki har da Ganduje, domin nan ba da dadewa ba APC za ta balle ta rabu gida biyu, saboda tana rungumar mutane masu tunani daban-daban.
“Na fadi haka, kuma ina sake maimaitawa: nan da watanni shida, duk wadanda suka koma APC za su dawo, kuma PDP za ta farfado da karfi don kwace mulki a 2027.”
A wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin ta hannun sakataren yada labaransa, Edwin Olofu, shugaban jam’iyyar APC na kasa ya yi watsi da ikirarin da cewa, hakan ba zai yi wu ba.
Ganduje ya ce maimakon ya koma PDP, Lamido ne zai koma APC nan ba da jimawa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp